Musulmi Na Hakika Ku Gayi Masa "Mu ba yan tafi kai-tsaye bane, A'a dole sai mun Jona da Manzon Allah._Inji Muhd Bala Afuwa

 


JAN HANKALI GA DR ABDUL AZIZ BAUCHI....


Tare da dukkan girmamawa, cikin bayanan da kuka saki akan wani faifan bidiyon waƙa da su Ali Nuhu suka yi, mai taken wa zai baka bayan Annabi?.


Daga abinda na saurara, maganar gaskiya na raina Usulubin da Dakta ya dauka yayi amfani da shi, don usulubin sam sam baiyi kama da na Malamai ba, balle kuma a cikin maluman Addini, kuma ma Dakta.


Allah ta'ala yana cewa a Alkur'ani mai girma.


 وما أرسلنك إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِينَ.

Ko da Dakta bai dubi girman wannan Rahmar da Allah ya aiko masa ba, a kalla bai kamata yace baya bukatar taimako daga gare ta.


بسم الله الرحمن الرحيم .


 لِّيَغۡفِرَ لَكَ ٱللَّهُ مَا تَقَدَّمَ مِن ذَنۢبِكَ وَمَا تَأَخَّرَ وَيُتِمَّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَيۡكَ وَيَهۡدِيَكَ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا.

In Dakta ya nazarci wannan Ayar, zai san cewa Annabi Muhammad (S) ba Ordinary mutum bane, Naturally daga Allah haka yake, banda ruwayoyi da suka zo dangane da falalarsa, banda wurare da dama da Allah yaita kambama Annabinsa yana masa kirari, da irin ambaton sa da yayi a Alkur'ani. 


Ga wasu shaidu kamar haka.


( وَمَا مُحَمَّدٌ إِلَّا رَسُولٌ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهِ الرُّسُلُ أَفَإِن مَّاتَ أَوْ قُتِلَ انقَلَبْتُمْ عَلَىٰ أَعْقَابِكُمْ وَمَن يَنقَلِبْ عَلَىٰ عَقِبَيْهِ فَلَن يَضُرَّ اللَّـهَ شَيْئًا وَسَيَجْزِي اللَّـهُ الشَّاكِرِينَ). "سورة آل عمران، آية: 144".


(مَّا كَانَ مُحَمَّدٌ أَبَا أَحَدٍ مِّن رِّجَالِكُمْ وَلَـكِن رَّسُولَ اللَّـهِ وَخَاتَمَ النَّبِيِّينَ وَكَانَ اللَّـهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمًا). "سورة الأحزاب، آية: 40".


(وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَآمَنُوا بِمَا نُزِّلَ عَلَى مُحَمَّدٍ وَهُوَ الْحَقُّ مِن رَّبِّهِمْ كَفَّرَ عَنْهُمْ سَيِّئَاتِهِمْ وَأَصْلَحَ بَالَهُمْ). "سورة محمد، آية: 2".


(مُّحَمَّدٌ رَّسُولُ اللَّـهِ وَالَّذِينَ مَعَهُ أَشِدَّاءُ عَلَى الْكُفَّارِ رُحَمَاءُ بَيْنَهُمْ تَرَاهُمْ رُكَّعًا سُجَّدًا يَبْتَغُونَ فَضْلًا مِّنَ اللَّـهِ وَرِضْوَانًا سِيمَاهُمْ فِي وُجُوهِهِم مِّنْ أَثَرِ السُّجُودِ ذَلِكَ مَثَلُهُمْ فِي التَّوْرَاةِ وَمَثَلُهُمْ فِي الْإِنجِيلِ كَزَرْعٍ أَخْرَجَ شَطْأَهُ فَآزَرَهُ فَاسْتَغْلَظَ فَاسْتَوَى عَلَى سُوقِهِ يُعْجِبُ الزُّرَّاعَ لِيَغِيظَ بِهِمُ الْكُفَّارَ وَعَدَ اللَّـهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ مِنْهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْرًا عَظِيمًا). "سورة الفتح، آية: 29".


(وَإِذْ قَالَ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ يَا بَنِي إِسْرَائِيلَ إِنِّي رَسُولُ اللَّـهِ إِلَيْكُم مُّصَدِّقًا لِّمَا بَيْنَ يَدَيَّ مِنَ التَّوْرَاةِ وَمُبَشِّرًا بِرَسُولٍ يَأْتِي مِن بَعْدِي اسْمُهُ أَحْمَدُ فَلَمَّا جَاءَهُم بِالْبَيِّنَاتِ قَالُوا هَـذَا سِحْرٌ مُّبِينٌ). "سورة الصف، آية: 6".


Ammai sai Dakta yace baya bukatar taimako daga Manzon Allah, a inda Dakta ya bada Maluma tare da kunya a Idon daliban ilmi, sai yace Annabi yace muce mu roki Allah in muna da bukata 😂.


To yanzu anan, wanene ya haska maka Allah ta'ala? Na san Dakta zaice Annabi ne, to ashe Annabin ya taimaka maka, kuma har ya baka wata hanya da zata kaika ga Allah, to idan Dakta ya ɓata a wurin kaiwa ga Allah, gashi a baya yace baya bukatar taimakon Annabi, tambaya! Wa zai sake dora shi a hanya?.


Duk Maluman da muke da su, da irin biyayyar da muke musu, muna musu ne saboda idaniyar mu bata iya riskar Manzon Allah, kuma muna da amincin zasu kaimu ga Manzon Allah, da ace munzo zamani daya da Annabi, tabbas da tare damu daku Dakta zamu koma ga Annabi don mu sha daga mabubbugar da Allah ta'ala ya aiko mana, saboda haka mu ba wadda zai bamu sai Annabi, saboda Annabi shi ya san Allah, da yadda ake bautar Allah.


Mu ba yan tafi kai-tsaye bane, A'a dole sai mun Jona da Manzon Allah.


Fatan Dakta zai riski sako na, Nagode.


Muhd Bala Afuwa

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post