MUNA TAYA MUMINAI MURNAR WANNAN RANAR MAI ALBARKA




A irin wannan ranar ta 17 ga Watan Ramadan na Shekara ta 2 bayan Hijira aka Gwabza Yakin nan da Ya Shahara a Duniyar Tarihi Wato Yakin Badar. Yakin da Allah ya bawa Muminai Nasara ta Zahiri da ta Badini,  Kuma Allah ya Kunyata Mushrikan Quraishawa da Sauran Masu  mara Musu baya  wajan ganin Bayan Kiran Ma'aiki (S) . Yakin Badar Yaki ne da a duk Ma'aunan Duniya bata yanda za ayi Muminai suyi Galaba, domin kuwa basuda Karfin yawa bare Kuma na Makamai,  Kuma ba ma sun fito ne da Nufin yin Yaki ba. Sun Fito ne da nufin tsare Ayarin kayan Mushrikan Makka da suka samu labarin Abu Sufyan ya biyo ta Madina da Kayan. Amma kwatsam sai abin Ya Juya ya zama Yaki ,ga shi Kuma a cikin Watan Ramadan ne Kuma ga Matsanancin Zafin Rana.


Su kuwa Mushirikan Makka sun Fito ne da fushi da kuma muggan makamai, ga kuma Yawan Mayaka da sun nunka na Muminai Yawa sau wajan Uku, domin adadin Muminai 313 ne, Mushrikan Kuraishawa kuwa sun Kusa Mayaka Dubu.


Ranar BADAR ,rana CE ta farin ciki abisa nasarar Rundunar Allah akan ta shedan !


Ranar Badar !Rana CE da rundunoni biyu suka hadu ! Rana ce dauwamammiya a tarihin musulunci da makomar Dan Adam .


"ولقد نصر كم الله ببدر وانتم اذلة فاتقوا الله لعلكم تشكرون" (١٢٣)


سورة ال عمران


Kuma Hakika Allah Ya baku Nasara a Badar Alhali Kuna raunana, Saboda haka Kuji Tsoron Allah ko zaku Zama Masu Godiya. 


Tarihin Badar na tunatar damu gwagwarmaya tsakanin gaskiya da bata ! Tsakanin adalci da zalunci !


 Samun nasarar da Manzon Allah (s) ya yi bayan hijirarsa daga Makka zuwa Madina, da kuma irin karɓar da mutanen Madina suka yi masa ya sanya kafiran Makkan cikin halin damuwa da kuma kara gaba da shi. Don haka suka fara tunanin hanyar da za su bi wajen kawo ƙarshen wannan addini na Musulunci da kuma wanda ya kawo shi (Annabi). Don cimma wannan manufa, kafiran Makkan da 'yan koransu suka fara kawo hare-hare ga yankunan da suke kusa da garin Madinan da kuma lalata kayayyakin gonakin musulmi da kuma ɗiban 'ya'yan itatuwan bishiyoyin musulman.


Ganin irin wannan shiri na makirci da kafiran suke wa musulmin da kuma Musuluncin ya sa Manzon Allah (s) ya ƙuduri aniyar kai hari wa wasu hanyoyin da kafiran suke samun kuɗaɗen shigan da suke amfani da su wajen ƙulla irin waɗannan makirce makirce. A ɓangare guda kuma kafiran Makka suna nan suna ta shirye-shiryen soji don kawo gagarumin hari wa musulmi da kuma murƙushe su. Kafiran dai sun iya tara rundunar soji da ta kai mutane 1000, da ta haɗa da raƙuma 700 da kuma dawaki 100, don aiwatar da wannan ƙuduri na su.


Koda wannan labari ya zo wa Manzon Allah (s) sai shi ma ya shirya rundunarsa ta mutane 313 da nufin fuskantar kafiran, inda suka fito daga garin Madinan don taryar kafiran a waje. Koda sojojin musulmai suka iso wani guri da ake ce ma Badar, sai Manzon Allah (s) ya umurce su da su dakata a gurin su jira isowar sojojin kafiran. Koda kafiran suka iso wajen sai Manzon Allah (s) ya tura Ammar bn Yasir da Abdullah bn Mas'ud don su je su leƙo asirin kafiran da kuma irin ƙarfin da suke da shi don a san yadda za a ɓullo musu. Inda waɗannan sahabbai suka je kuma suka dawo da labarin da suka samo.


Kafin a fara wannan yaƙi dai Manzon Allah (s) ya miƙa tutan rundunarsa ne ga Amirul Muminina Aliyu bn Abi Talib (a.s).


Wannan yaƙi dai na Badar an fara shi ne a ranar 17 ga watan Ramalana shekara ta biyu bayan hijira. A wancan lokacin dai, larabawa suna da wani tsari na yaƙi da suke bi, shi ne kuwa kafin a fara yaƙin wasu dakaru sukan fito su gwabza tsakaninsu. Don haka a yaƙin Badar ɗin ma hakan ne ta faru.


Koda ɓangarorin biyu (wato bangaren gaskiya da shiriya karkashin jagorancin Manzon Allah (s) da kuma bangaren ƙarya da ɓata ƙarƙashin jagorancin Abu Sufyan) suka fuskanci juna, sai wasu kafirai guda uku, wato Walid, Shaybah da kuma Utbah suka fito don tinƙarar musulmin. A nan wasu sahabbai Ansarawa guda uku suka fito, sai suka ki amincewa da su suka ce ai ba sa'oinsu ba ne. Sai Manzon Allah ya umurci Ali bn Abi Talib, Hamzah da kuma Ubaydah da su fito su tunƙare su. Inda ya ce wa Aliyu ya kama Walid, Hamzah kuwa ya kama Shaybah shi kuma Ubaydah ya kama Utbah. Koda aka fara gwabzawa, nan take Aliyu ya kashe Walid, Hamzah ma ya sare Shaybah, shi kuwa Ubaydah Utbah ya ji masa ciwo, nan take Aliyu da Hamzah suka kawo masa ɗauki, suka ƙarasa Utbah.


Ta haka ne sojojin Musulmi suka fara samun nasara, tsoro da fargaba kuma ya shiga zukatan dakarun kafirci, inda wuri ya ruɗe, daga ƙarshe dai musulmi suka sami nasara, suka kashe da dama daga cikin kafirai da taimakon Aliyu bn Abi Talib wanda ya kashe mafi yawa daga cikin kafiran da aka kashe a yaƙin. Kafirai suka watse suka gudu musulmi suka bi su suka ɗibi ganima da kuma fursunonin yaƙi suka dawo gida.


Wannan dai ita ce nasarar farko da musulmi suka samu a ɓangaren soji akan kafirai.


        --Jawad Adamu Tsoho

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post