KUYANGAR SAYYIDAH ZAHRAH (S. A) MAI MAGANA DA ALQUR'ANI

 


WACECE NANA FIDDAH 'YAR GARIN NAUBAH  (S. A)  ???


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KUYANGAR SAYYIDAH ZAHRAH (S. A) MAI MAGANA DA ALQUR'ANI 


Shi dai yankin Naubah dake Afrika yanki ne dake  gabas da kogin Nilo tsakanin Aswan da Dinkalah a (Sudan). Yankin Naubah bangare biyu ne, wato akwai Naubah ta gangare da Naubah ta tudu. 


Naubah ta gangare ita ce  yankin dake tsakanin Masar da Sudan, da kuma kwarin Hulafa'a. 


Ita kuma Naubah ta tudu ita ce yankin dake Sudan. Muslimci ya shigo gun ne a qarnin farko na Hijrar Annabi (S. A. W. W) .


Su dau Naubawa sun shahara da kyawawan dabi'u ko siffofi ababen yabo, wanda ke nuna suna da sauran kyawawan al'adu wadanda aka halacci mutane a kanta. 


Daga cikin kyawawan dabi'unsu sun hada da :


Zaman lafiya, 


Wadatuwa da kadan, 


Jaruntaka da taimako, 


Girmama al'adun wasu jama'a da gargajiyarsu da kuma, 


Riqon amana da yin aiki bisa Ikhlasi .


Ya zo cikin cikin littafin Al-Isabah na Ibn Hajar Al-Asqalani ya ambato cewa an riwaito daga Imam Sadiq daga iyayensa daga Aliyu (A. S) cewa Manzon Allah (S. A. W. W) ya bawa 'yarsa Fatima mai aiki sunanta Fiddah 'yar garin Naubah don ta riqa taimaka mata da aiki. Kuma ya sanar da ita wata addu'ah wacce take yin addu'ah da ita. Sai wata rana Fatimah tace mata kullum za ta riqa yi musu waina (Masa). Sai tace a'a, za ta riqa kwaba qulli kuma ta riqa yiwo mata Itace.


Wata rana Nana Fiddah ta tafi yiwo Itace, bayan ta gama yayin da tazo dauka sai ta kasa, sai tayi wannan addu'ah wacce Annabi (S. A. W. W) ya koya mata. Ga ta kamar haka :


" YAA MAKADAICI WANDA BABU WANI KAMARSA. KANA IYA KASHE KOWA KUMA KANA BISA AL-ARSHINKA MADAIDAICI.  GYANGYADI BA YA KAMA SHI BALLE BACCI. "


Sai ga wani Balaraben Qauye yazo ya dauki wannan damin Itacen ya kai mata har zuwa qofar gidan Sayyidah Fatimah (S. A). 


YADDA TAKE MAGANA DA ALQUR'ANI 


Don jin yadda take magana da Al-Qur'ani sai ku biyo mu kamar haka :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


أَبُو الْقَاسِمِ الْقُشَيْرِيُّ فِي كِتَابِهِ قَالَ بَعْضُهُمْ‏ انْقَطَعْتُ فِي الْبَادِيَةِ عَنِ الْقَافِلَةِ فَوَجَدْتُ امْرَأَةً فَقُلْتُ لَهَا مَنْ أَنْتِ ?


Abu Qasim Al-Qushairiy ya kawo cikin littafinsa cewa, sashensu yace : " Mun tafi cikin wani Qauye cikin wani Ayari sai muka sami wata mata, sai nace mata, ke wacece ?


 فَقَالَتْ : " وَ قُلْ سَلَامٌ فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ‏."


Tace : " KACE SALAMUN, DA SANNU ZA KA SANI (wato ka fara da sallama). "


 فَسَلَّمْتُ عَلَيْهَا فَقُلْتُ 

مَا تَصْنَعِينَ هَاهُنَا ?


Sai nayi mata sallama kuma nace, me kike yi anan  ?


 قَالَتْ‏: " مَنْ يَهْدِ اللَّهُ‏ فَلَا مُضِلَّ لَهُ‏."


Tace : " AI DUK WANDA ALLAH YA SHIRYAR BABU MAI 'BATAR DASHI. "


 فَقُلْتُ:  أَ مِنَ الْجِنِّ أَنْتِ أَمْ مِنَ الْإِنْسِ ?


Sai nace : Ke kuwa daga Aljannu kike ko kuma daga cikin mutane 


 قَالَتْ‏: " يا بَنِي آدَمَ خُذُوا زِينَتَكُمْ‏"


Sai tace : " YAA KU 'YAN ADAM KU RIQI ADONKU (ma'ana kayi abinda ke gabanka kawai). "


 فَقُلْتُ:  مِنْ أَيْنَ‏

أَقْبَلْتِ ?


Sai nace, " TO, DAGA INA KIKA FITO ? "


قَالَتْ‏: " يُنادَوْنَ مِنْ مَكانٍ بَعِيدٍ. "


Tace: " SUNA KIRA DAGA GURI MAI NISA (gurin dana fito yana da nisa). "


 فَقُلْتُ:  أَيْنَ تَقْصِدِينَ ?


Nace, yanzu kuma ina kika nufa  ?


 قَالَتْ‏: " وَ لِلَّهِ عَلَى النَّاسِ حِجُّ الْبَيْتِ‏. "


Tace : " AN WAJABTAWA MUTANE HAJJI (ma'ana dole na koma inda na fito). "


 فَقُلْتُ : مَتَى انْقَطَعْتِ?


Sai nace, yaushe kike wannan guri (bayan kika kasa komawa inda kika fito)  ?


 قَالَتْ‏ : " وَ لَقَدْ خَلَقْنَا السَّماواتِ وَ الْأَرْضَ‏ ...

فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ‏ "


Sai tace : " HAQIQA ALLAH YA HALICCI SAMMAI DA QASSAI .......CIKIN KWANA SHIDA. "


فَقُلْتُ:  أَ تَشْتَهِينَ طَعَاماً ?


Sai nace, kina sha'awar abinci ? 


فَقَالَتْ‏ : "وَ ما جَعَلْناهُمْ جَسَداً لا يَأْكُلُونَ الطَّعامَ‏ "


Tace : " AI BAMU SANYA SU JIKI (kamar Mala'iku) BA SA CIN ABINCI BA. "


فَأَطَعَمْتُهَا ثُمَّ قُلْتُ هَرْوِلِي وَ لَا تَعَجَّلِي.


Sai na ciyar da ita sannan  nace, kiyi a hankali kada kiyi gaggawa. 


 قَالَتْ‏: " لا يُكَلِّفُ اللَّهُ نَفْساً إِلَّا وُسْعَها "


Tace : " ALLAH BA YA 'DORAWA RAI (wani abu) FACE IYAWARTA. "


فَقُلْتُ:  أُرْدِفُكِ?


Sai nace, nayi miki rakiya  (wato na dauke ki kan abin hawana na raka ki)  ?


 فَقَالَتْ‏: " لَوْ كانَ فِيهِما آلِهَةٌ إِلَّا اللَّهُ لَفَسَدَتا."


Sai yace : " DA DAI CIKINSU (sammai da qassai) AKWAI WANI ABIN BAUTA (wanda ba Allah ba) DA SUN RUGUJE. " (Ma'ana kasancewa mutum biyu wadanda ba Muharramai ba akan abin hawa na da matsala). 


 فَنَزَلْتُ فَأَرْكَبْتُهَا

 

Sai na sauka (daga kan abin hawan nawa) ita ta hau. 


 فَقَالَتْ‏: " سُبْحانَ الَّذِي سَخَّرَ لَنا هذا "


Sai tace : " TSARKI YA TABBATA GA (Allah) WANDA YA HORE MANA WANNAN (abin hawa mai sauqaqa mana wajen tafiya da daukar kaya). "


فَلَمَّا أَدْرَكْنَا الْقَافِلَةَ قُلْتُ أَ لَكِ أَحَدٌ فِيهَا?


Yayin da muka riski wasu  ayari sai nace, shin ko kina da wani (wanda kika sani) a cikinsu ? 


 قَالَتْ‏: " يا داوُدُ إِنَّا جَعَلْناكَ خَلِيفَةً فِي الْأَرْضِ‏[16]. وَ ما مُحَمَّدٌ إِلَّا رَسُولٌ‏[17] يا يَحْيى‏ خُذِ الْكِتابَ‏[18] يا مُوسى‏ إِنِّي أَنَا اللَّهُ‏[19] .


Tace : " YAA DAWUDA, LALLE MUN SANYA KA HALIFA CIKIN QASA . KUMA MUHAMMADU BAI KASANCE BA FACE MANZO. YAA YAHYA, KA RIQE LITTAFI. YAA MUSA,  LALLE NINE ALLAH. " ( Ma'ana ai yanzu kaine wanda zai jagorance ni domin babu wanda na sani daga cikinsu. Kuma kai dan saqo ne wanda Allah ya aikoka gare ni don taimaka mini. Kuma Allah nanan tsakaninmu yana sa ido a kanmu). 


فَصِحْتُ بِهَذِهِ الْأَسْمَاءِ فَإِذَا أَنَا بِأَرْبَعَةِ شَبَابٍ مُتَوَجِّهَيْنِ نَحْوَهَا فَقُلْتُ مَنْ هَؤُلَاءِ مِنْكِ?


Tayi amfani da wadannan sunaye, sai ga wasu samari guda hudu sun fuskanto mu ta bangarenta. Sai nace, su wanene wadannan a gare ki  ?


 قَالَتْ‏: " الْمالُ وَ الْبَنُونَ زِينَةُ الْحَياةِ الدُّنْيا[20] "


Tace : " ITA DUKIYA DA 'YA'YA ADO NE NA RAYUWAR DUNIYA. " (Ma'ana ai 'ya'yanta ne). 


فَلَمَّا أَتَوْهَا قَالَتْ‏ " يا أَبَتِ اسْتَأْجِرْهُ إِنَّ خَيْرَ مَنِ اسْتَأْجَرْتَ الْقَوِيُّ الْأَمِينُ‏[21]"


A yayin da suka iso gare ta sai tace : " YAA BABANA, KA BA SHI LADA (na wannan aiki da yayi), LALLE MAFI ALKHAIRIN WANDA ZA KA BAWA LADAN NAN MAI QARFIN (imani ne) KUMA AMINTACCE (marar cin amana). "


 فَكَافُونِي بِأَشْيَاءَ.


Sai suka wadata ni da wasu abubuwa. 


 فَقَالَتْ‏: " وَ اللَّهُ يُضاعِفُ 

لِمَنْ يَشاءُ[22] "


Sai tace : " KUMA ALLAH NA NINNINKAWA GA WANDA YASO (wato ku qara masa). "


فَزَادُوا عَلَيَّ فَسَأَلْتُهُمْ عَنْهَا فَقَالُوا هَذِهِ أُمُّنَا فِضَّةُ جَارِيَةُ الزَّهْرَاءِ ع مَا تَكَلَّمَتْ مُنْذُ عِشْرِينَ 

سَنَةً إِلَّا بِالْقُرْآنِ. 


Sai suka qara min. Sai na tambaye su game da ita, sai suka ce : " Wannan mahaifiyarmu ce Fiddah, kuyangar Zahrah) S. A). Tsahon shekaru ashirin kenan ba ta magana sai da Al-Qur'ani. 


(1) الضحى: 5.


(2) الزخرف: 89.


(3) لم نجد بهذا اللفظ آية في القرآن و الموجود فيه: الزمر: 38 وَ مَنْ يَهْدِ اللَّهُ فَما لَهُ مِنْ مُضِلٍ‏.


(4) الأعراف: 29


.(1) فصّلت: 44.


(2) آل عمران: 91.


(3) ق: 37 بزيادة: وَ ما بَيْنَهُما. بعد الْأَرْضَ‏.


(4) الأنبياء: 8.


(5) البقرة: 286.


(6) الأنبياء: 22.


(7) الزخرف: 12.


(8) ص: 25.


(9) آل عمران: 138.


(10) مريم: 13.


(11) طه: 11 و 13.


(12) الكهف: 44.


(13) القصص: 26.


(14) البقرة: 263.


(15) الحجر: 43 و 44.


 

بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏43، ص: 88


Wannan ita ce Nana Fidda (S. A) wacce tayi hidima ga Sayyidah Zahrah (S. A), sai Allah (T)  ya albarkaceta da baiwar ilimi har ta kai duk wata maganar da za tayi ba ta yi sai da ayoyin Al-Qur'ani.  Duk wanda ya riqi iyalan gidan Annabi Muhammad (S. A. W. W) kuma yake yi musu hidima, to, zai azurtu da ilimi kamar ruwan sama ☔. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


          (08137925034)


17th January, 2023/  25th Jimada-Sani, 1444

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post