KO KASAN MATAKAN DA AKE BI KAFIN A KAI GA SAKIN AURE?

  A yau mun wayi gari al'ummar mu ta arewacin  wannan kasa ta mu, yawaitar sakar aure ya zamo ruwan dare, ta yadda da za'a kiyasata yawaitar mace-macen aure babu abin da zamu ce sai dai mu ce innalilla waa inailahirrjiun. 


Ko da ya ke da yawan al'ummar mu musamman samari kowa da ya farka yaga ya na da yan chanji, babu abin da ya ke hankoro face shi dai yaga ya yi aure, haka ma itama budurwa da ta fara dagowa kawai ita burin ta ayi mata aure musamman idan aka yi rashin sa'a yarin ya ce me yawan kallan fina-finai barkatai musamman na soyayya na cikin gida da na waje, wanda wannan ya na tasirantuwa a kwakwalan samari da yan mata, kai a wani lokacin ma har zawarawa. Ta yadda kallan wadannan fina-fina tasirin sa, takai ga su masu kallan fina-finai suna kaddara su a matsayin rayiwar aure ta zahiri a yayin da suka yi aure, su suna ganin duk wani irin jin dadi da alatu da walwala da gidaje da motoci masu tsada suna ganin wannan rayiwar da ake nunawa a fina-finai haka suke sauwalawa ita za su a rayiwar auran su ta zahari tare da cewar sun manta wasan kwaikwayo ne (Drama). 


Sabo da haka ba mu na nuni da cewar yin aure ga da namiji ko 'ya mace illah ba ne a'a hakan ya na da matukar muhimmanci a rayiwa sai dai babban abin da ya hau kan wannan al' ummar tamu karancin sanin hukunce-hukunce auran da yadda za ayi zaman takewar auran, me ya kamata na yi a lokacin da matata ta yi min ba daidai ba. Wacce hanya zan bi dan kawar da irin abin da ke min cikin hikima da dabara. 


Hakama ta fuskacin matan suma waddanne dabaeu ya kamata mace ta bi a lokacin da mijin ta ya fatamata wanne mataki zan dauka ta hanyar nasiha da kwantar da kai domin kai ga nasara ta yadda ya da ce. sai ya zamana al'ummar mu mafi yawansamari da yan mata kai harma da zawarawan su jahilci zaman ta kewar auran yadda ya da ce da yadda addini ya tsaramana. 


Ko wannan mu hankoran mu shine yin auran domin mu huta muji da dadi kamar yadda masu kallan fina-finai suke gani a film. Tare da cewar sun manta shi kan kinkansan auran ibadane, ita ko duk abin da aka ce ibadane to dolane sai ka fahimci jarrabawa domin wannan jarrabawa shi zai baka damar karin samin lada a wurin Allah (T). Sabo da haka kar duka bangaren samari da yan mata su dauka cewar rayiwar aure rayiwace ta sharholiya idan ma mutum yana ganin haka to ya sauya. 


Haka kuma wajibine a duk lokacin da mutum ya  fara neman aure, *dolane a kansa ya nemi ilimi na zaman takewar aure da hukunce hukunce sa* da dabar baru na koyan zama da iyali. kamar yadda mutumin da zaije aikin hajji dola ne akan sa ko a kanta su san hukunce hukunce aikin hajji kafin tafiyar su kasa me tsarki. 


Amman dayawan mu a rayiwar mu ba ruwan mu da sanin hukunce hukunce aure da sanin  dabar baru na zamanta kewar aure. A a kawai a yi auran shine kawai burin mu. 


Ta ya ya ko aure za a samu yayi karko? Dolane ya zamana dukkan bangarorin biyun su jahilci hakkunan su na zaman takewar dole karshe ai ta samun mas'aloli karshe takai ga aure ya fara tangal tangal. 


Bugu da kari wasu ma tun a neman auran da yadda aka yi auran memakon a nemi yardar Allah da sa albarkasa ga wannan auran karshe an aiwatar da munanan aiyuka da Allah ya haramta a dasawa wannan auran fushin rabbil izzati karshe auran ya zamo babu albarka ko kuma a samu zuria mummunar zuriar da sai dai arinka cewa alawadai tir, me makon asamu zuria me albarka. Sabo da haka wadanne hanyoyi za mu bi dan kawar da ya waitawa sake sake da ke yawan faru a wannan nahiya ta mu? 


   Sannan wadanne hanyoyi na miji ya kamata ya bi kafin ya kai ga saki? 


Ku biyoni a kashi na biyu 

Daga taskar rubutun tukan

*Habib Nasrallah*


©Habib Nasrallah. 

Email.:habibrabiu81@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post