Wafatin Sayyida Khadija Da Abubuwan Da Suka Biyo Baya




Sayyida Khadija uwar gida ce a wajen Muhammad Rasulallah (Saww) kuma a ranar 10 ga watan Ramadan Allah ya mata rasuwa (Ta Koma Zuwa Ga Allah), shekara 10 kafin hijirar Annabi (Saww), bayan ɗan rashin lafiya da tayi. Shi zama na jaje yana daga cikin haƙƙoki na Ahlulbait, kuma ya kamata ya zama muminai su kasance suna farin ciki da farin cikin Ahlulbait sannan suyi bakin ciki da bakin cikin su. 


Imam Ja'afar Assadiq (As) Yana cewa; magoya bayan mu yanki ne daga gare mu, (wato Shi'ar mu yankin mu ne). An halicce su ne da sauran taɓon mu, abin da duk ya bata mana rai, suma yana bata musu, abin da ya faranta mana rai yana farantawa masoyan mu rai.


Kamar yadda muka yi bayani a 10 ga Ramadan, cikin irin wannan shekara ne ita Ummul Muminin Khadijatul Khubra tayi wafati! Bayan Abu Ɗalib ya koma ga Allah da kwana Arba'in da Biyar (45) itama Allah ya mata rasuwa!


Ita Sayyida Khadija Manzon Allah ya aure ta a matsayin Budurwa ce ba Bazawara ba, kamar yadda wasu suka rawaito cewa wai Annabi ya aure ta a matsayin Bazawara. Manzon Allah bai auri wata mata ba a lokacin da yake tare da Khadija ta haifa masa Ƴaƴa tare da shi. 


Kuma ita Sayyida Khadija ita ce farkon mace wanda ta fara karban musulunci, bayan Manzon Allah ya dawo daga kogon Hira da shi da ƙaninsa Amirul Muminin Aliyu (As) ya bayyana mata cewa ga sakon da aka isar mishi ya isar wa Al'umma inda kuma ya kira ta kuma ta amsa sakon. Shi kuma Sayyidi Aliyu daman tuntuni shi musulmi ne ya yi imani da Manzon Allah tun kafin saukar wahayi.


Sayyida Khadija ta taka rawa mai girman gaske a rayuwar Manzon Allah da tarihin musulunci, matace tsayayya jaruma wacce ta taimakawa Manzon Allah akan abin da Allah ya aiko shi akai. Dukiyar ta sadaukar wajen taimakawa Annabi da musulunci kuma al'umma musulmai. Ya ishe ta girman daraja da ta kasance uwa ga Sayyida Fatima Azzahara (As).


Ita kaɗaice Allah ya wanzar da zuriyar Manzon Allah ta tsatson ta sune Ahlulbait. Ance lokacin da ta kwanta rashin lafiyar da bata tashi ba, tace Ya Rasulullah ina rokon ka da cewa ka ɗauki wannan zamantakewa aure da muka yi na shekaru in na taƙaita wani haƙƙin ka wanda ban maka ba, ina rokon ka yafe min. Sai Manzon Allah yace Tun da na aure ki ban taba ganin wani abu ba sai Alkhairi daga gare ki, wannan shedane daga Sadiƙul Musaddik Muhammad Rasulallah.


Manzon Allah ya ƙara da cewa ban san komai daga gare ki ba sai taimaka da jure dukkan cutarwa, kuma kin bada duniyar ki (Sadaukar) gaba ki ɗaya don addinin Allah ya tabbata, don haka ba abin da zan ce kimi sai  dai Allah ya saka da Alkhairi. Kuma tun daga nan duniya Manzon Allah ya mata bishara da zai bata makullin aljanna. 


Sai Sayyida Khadija tace ya Rasulallah ina ma wasiyya da wannan, sai ta nuna Sayyida Zahra. Domin nan da wani lokaci kaɗan zata zama baƙuwa kuma marainiya a baya na, kuma kada wata mata Bakurashiya ta cutar da ita. Kada wani ya doketa kuma kada wani ya ɗaga murya akan ta, kuma bana son taga wani abin bakin ciki tare da ita.


Sayyida Khadija Itace farkon mace da ta gaskata Annabi, kuma itace wacce ta fara sallah a bayan Annabi aka yi jam'i da ita. Kuma itace farkon mace  da ta jajirce wajen kare Manzon Allah da dukiyarta wajen yaɗa wannan addini da taimakon raunana. Kuma ita ce farkon mace da imanin ta yakai na kamala, domin kamar yadda muka yi  bayani tana daga cikin mata hudu wanda Manzon Allah yayi bayanin su.


Manzon Allah yake cewa, mazaje sun kammala a imanin su da mutumtaka ɗin su , amma a mata Huɗu ne suka samu wannan kammala ɗin. Na farko itace Sayyida Asiya matar Fir'auna, na Biyu itace Sayyida Maryam Mahaifiyar Annabi Isa, na Uku itace Sayyida Khaidja matar Annabi, na Huɗu itace Sayyida Fatima (As) ɗiya ga Khadija. Manzon Allah yace wannan mata sun kammala a imanin su kuma sun kammala a mutumtaka ɗin su, sun kammala a kyawawan ɗabi'unsu.


Daga jawabin Sheikh Adamu Tsoho Jos wanda yayi ranar 10 ga watan Ramadan shekarar 1441/2020 a Hussainiyyatu Sheikh Zakzaky (H) Jos. 


*#HSZJ.*

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post