SU MUSULMAI NE KO AHLUS SUNNAH?


Tare da Yusuf Alhaji Lawan 


Allah madaukakin Sarki ya halicci halitta ne domin manufa kuma akwai tsari da yake so halittunsa su rayu akai. Cikin hikimarSa da tausayawarSa, ya zabi ya turo Annabawa domin su shiryatar da bayi zuwa ga tafarkinsa.


Saboda girmamawa da daukaka wannan al'umma, sai ya fifita mu da bamu fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (S.A.W). Yazo mana da shiriya da addinin gaskiya domin ya daukaka shi birbishin duk addinai koda mushrikai sun ki.


Muhimmin sako da yazo mana dashi shine Al-Qur'ani mai girma wadda ya kunshi komai da komai da Dan Adam ke bukata domin samun ingantacciyar rayuwa a duniya da kuma tsira gobe Kiyama.


"Lallai addini a wajan Allah shine Musulunci." Haka Allah yace a cikin Qur'ani. Duk wani da yazo da addini koma bayan Musulunci to ba za'a karba masa ba.


Na kan shiga cikin tunani mai zurfi idan na lura da yadda wasu bangare na al'ummar musulmi suke gudanar da nasu addinin ba tare da i'itirafi da kalmar musulunci ba a dukkan ayyukansu. Da wahala kaga suna amfani da kalmar Islam ko Musulunci a cikin al'amuransu ballantana kaga suna godiya wa Allah akan ni'imar musulunci.


Suna bayyana kansu a ko ina da cewa sunansu Ahlus Sunnah. Da suka tashi kafa kungiya sai suka saka mata suna Jama'atul Izalatul Bid'a wa Iqamatus Sunnah. Babu wata kalma dake nuna wannan kungiya a cikin musulunci take. Suka kafa wata kungiya sunanta Jama'atu Ahlus Sunnati Lid Da'awati Wal Jihad. Idan malamansu zasu rubuta littafi, sai su saka masa suna Minjahus Sunnah, Fiqhus Sunnah ko Aqidatu Ahlus Sunnah ba Minjahul Islam ko Fiqhul Islam ba.


Da zasu bude gidan talabijin sai suka saka masa suna Sunnah TV. Sai kaji sunce Malaman Sunnah, Masallacin Ahlus Sunnah, Allah ya raya akan Sunnah, Sunnah Sak, Baraden Sunnah, Asadus Sunnah da sauransu.


Idan mutum yayi nazari da kyau, zai lura da cewa kullum basu amfani da kalmar musulunci alhali su Musulmai ne sai dai Sunnah wadda hakan bashi da asali a musulunci.


Na karanta Al-Qur'ani mai tsarki daga farko zuwa karshe, ban ga aya guda daya ba da Allah (S.W.T) yayi umarni da cewa Musulmai su zama Ahlus Sunnah ba ko kuma kalmar Sunnah ta zama ma'auni na rarrabewa tsakanin musulmi da wadda bashi ba. Daga Hadisai na Annabi Muhammadu (S.A.W) da tarihin Musulunci wadda ido na ya kai gare su, banci karo da wani wuri da Annabi Muhammadu (S.A.W) ya sakawa wani Sahabi laqabi da Ahlus Sunnah ba, ko yayi umarni da hakan. Ko kuma aka ruwaito wani Sahabi ya sawa kansa suna Ahlus Sunnah ba ballantana a sami umarni da cewa komai na musulmi a ambace shi da kalmar Sunnah ba.


Lokaci yayi da kowa ya kamata ya bayyana kansa a matsayin Musulmi kuma a ga musulunci a sunansa da ayyukansa. Karfin al'ummar musulmi yana cikin hadin kai, rauni kuma na cikin rarraba.


Allah ya fahimtar damu hakikanin musulunci kuma ya bamu ikon dabbaqa shi a rayuwarmu ta yau da gobe. Allah ya hada kan al'ummar musulmi domin cigaban addini, ya yafe mana kurakurenmu, ya bamu ikon sakin ganye mu kama tushe don darajar Annabi Muhammadu Rasulillahi (S.AW.)

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post