KUMA KU CIKA AZUMI ZUWA DARE !!!

 


KUMA KU


KUMA KU CIKA AZUMI ZUWA DARE   !!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


AIKIN UMAR BN KHADDAB YA QARYATA HADISIN GAGGAUTA BUDE BAKI ๐Ÿ‘„ 


Ni dai ban san wanne dalili yasa mutane suka qirqiri qarya suka jinginata ga Annabi (S. A. W. W) ba, ko dai hakan na nuna salo ne na yin yaqi da koyarwarsa ? Lalle irin wannan aiki na cin karo da ayoyin Al-Qur'ani wanda hakan ke nuna fito-na-fito ne da dokokin Allah (T). 


Cikin Al-Qur'ani mai girma Allah yayi umarci game da cika azumi zuwa dare, amma sai aka ce wai gaggauta baki na  daga cikin dalilan dake sa mutum ya dawwama cikin alkhairi, hakan kuwa qaryata ayar nan ce mai cewa :


๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ


".......ูˆَูƒُู„ُูˆุง ูˆَุงุดْุฑَุจُูˆุง ุญَุชَّู‰ ูŠَุชَุจَูŠَّู†َ ู„َูƒُู…ُ ุงู„ْุฎَูŠْุทُ ุงู„ْุฃَุจْูŠَุถُ ู…ِู†َ ุงู„ْุฎَูŠْุทِ ุงู„ْุฃَุณْูˆَุฏِ ู…ِู†َ ุงู„ْูَุฌْุฑِ ุซُู…َّ ุฃَุชِู…ُّูˆุง ุงู„ุตِّูŠَุงู…َ ุฅِู„َู‰ ุงู„ู„َّูŠْู„ِ................"


" ........KUMA KU CI KU SHA HAR SAI FARIN ZARE YA BAYYANA DAGA BAQIN ZARE NA DAGA ALFIJR, SA'AN NAN KU CIKA AZUMI ZUWA DARE........ "


(BAQARA, AYA TA 187)


Bayyanar farin zare daga baqin zare shine ketowar Alfijr na gaskiya (SAADIQ), dare kuma shine asalin dare wanda ba ya daukar tawili, wato abinda zai amsa suna dare ba tare da ba shi wani suna na dabam ba. Duk da cewa maganar gaggauta bude baki ta zo cikin littafai da dama irin su Bukhari da Muslim, amma mun zabi mu kawo wanda yazo ne cikin littafin Imam Malik mai suna MUWADDA domin gwama shi da hadisin da ya biyo bayansa nan take (Immediately) bayan kawo hadisin. 


Wadannan riwayoyi an kawo su ne cikin Babin dake magana kan gaggauta buda baki kamar yadda za mu gan shi kamar haka :


๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ


﴿ ุจุงุจ ู…ุง ุฌุงุก ููŠ ุชุนุฌูŠู„ ุงู„ูุทุฑ ﴾ 


628- ูˆَุญَุฏَّุซَู†ِูŠ ، ุนَู†ْ ู…َุงู„ِูƒ ، ุนَู†ْ ุนَุจْุฏِ ุงู„ุฑَّุญْู…َู†ِ ุจْู†ِ ุญَุฑْู…َู„َุฉَ ุงู„ْุฃَุณْู„َู…ِูŠِّ ، ุนَู†ْ ุณَุนِูŠุฏِ ุจْู†ِ ุงู„ْู…ُุณَูŠَّุจِ ، ุฃَู†ّ ุฑَุณُูˆู„َ ุงู„ู„َّู‡ِ ุตَู„َّู‰ ุงู„ู„َّู‡ُ ุนَู„َูŠْู‡ِ ูˆَุณَู„َّู…َ ู‚َุงู„َ : " ู„َุง ูŠَุฒَุงู„ُ ุงู„ู†َّุงุณُ ุจِุฎَูŠْุฑٍ ู…َุง ุนَุฌَّู„ُูˆุง ุงู„ْูِุทْุฑَ " .


An ba ni labari daga Malik, daga Abdurrahman Bn Harmalata Al-Aslamiy, daga Sa'eed Bn Musayyib, daga Manzon Allah (S. A. W. W) ya ce :


" MUTANE BA ZA SU GUSHE TARE DA ALKHAIRI BA  MATUQAR SUNA GAGGAUTA BUDA BAKI. "


Na'am, da shike Qur'ani dai ya ambata mana ne cewa mu cika azumi zuwa dare amma bai nuna mana cewa farkonsa ne ko tsakiyarsa ko kuma qarshensa ba, saboda haka za a iya shan ruwa matuqar ya tabbata dare ya yi. 


Amma wannan riwaya da aka samu daga Manzon Allah (S. A. W. W) mai kwadaitarwa game da gaggauta bude baki sai ya nuna mana farkon dare ne ba tsakiya ko qarshensa ba. Saboda haka ba za mu qaryata wannan riwaya ba, amma dai za muyi amfani da aikin da wasu su kayi wajen fassara wannan aya aikace. 


Riwayar kuma ita ce :


629- ูˆَุญَุฏَّุซَู†ِูŠ ، ุนَู†ْ ูˆَุญَุฏَّุซَู†ِูŠ ، ุนَู†ْ ู…َุงู„ِูƒ ، ุนَู†ْ ุงุจْู†ِ ุดِู‡َุงุจٍ ، ุนَู†ْ ุญُู…َูŠْุฏِ ุจْู†ِ ุนَุจْุฏِ ุงู„ุฑَّุญْู…َู†ِ ، ุฃَู†َّ ุนُู…َุฑَ ุจْู†َ ุงู„ْุฎَุทَّุงุจِ ، ูˆَุนُุซْู…َุงู†َ ุจْู†َ ุนَูَّุงู†َ " ูƒَุงู†َุง ูŠُุตَู„ِّูŠَุงู†ِ ุงู„ْู…َุบْุฑِุจَ ุญِูŠู†َ ูŠَู†ْุธُุฑَุงู†ِ ุฅِู„َู‰ ุงู„ู„َّูŠْู„ِ ุงู„ْุฃَุณْูˆَุฏِ ู‚َุจْู„َ ุฃَู†ْ ูŠُูْุทِุฑَุง ، ุซُู…َّ ูŠُูْุทِุฑَุงู†ِ ุจَุนْุฏَ ุงู„ุตَّู„َุงุฉِ ูˆَุฐَู„ِูƒَ ูِูŠ ุฑَู…َุถَุงู†َ " .


An bani labari daga Malik, daga Ibn Shihaab, daga Humaid Bn Abdurrahman cewa :


" LALLE UMAR 'DAN KHADDAB DA USMAN BN AFFAN SUN KASANCE (su biyun) SUNA SALLATAR MAGRIBA YAYIN DA SUKE SAURARON (shigowar ) DARE MAI DUHU KA FIN SU SHA RUWA, SA'ANNAN SHU SHA RUWA (bayan sunyi sallar Magrib),  KUMA HAKAN (suna yinsa ne) CIKIN RAMADAMA. "


Darasin dake cikin wannan riwaya shine, a aikace dai su Umar sun fassara wannan aya ne da  cewa in har sunnar Annabi (S. A. W. W) dole ya zama bayan sallar Magrib ne ake sha.


Idan kuma ya tabbata kafin cikar dare ake shan ruwa, to, za ace su Umar Bn Khaddab da Usman Bn Affan ba sa koyi da Manzon Allah (S. A. W. W).  Idan kuma ya tabbata bayan sallar Magrib ake shan ruwa, to,   wannan riwaya ta zama qirqirarriya wacce aka qirqirota, ko kuma dai gaskiya ce amma ba ana nufin shan ruwa ne a irin wannan lokaci ba.


Saboda haka sai a kiyaye don kada aikin wasu yayi sanadin bata aikin da Allah ya wajabta maka. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍๐ŸผAdo Isah Guda.


           (08137925034)


26th March, 2023/  4th Ramadan, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post