Azumin Masu Sana'ar Tafiye-Tafiye kamar Direban mota ko wanda ya aikinsa ya dogara da yin tafiye-tafiye

 MA'ASUMA NIGERIA NEWS UPDATE


✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey 


Wanda Tafiye-tafiye ne sana'arsa kamar Direban mota ko wanda ya aikinsa ya dogara da yin tafiye-tafiye wajibi ne suyi Azumi , amma idan ya zama sunyi tafiya ta daban wacce bata shafi aikinsu ba to anan dole suyi ƙasaru a Sallah kuma dole su ajiye Azumi , sun zama kamar waninsu .


Ma'ana da ace wani uzuri daban da bai shafi harkarsu ta Tuƙin Mota ba zai sa suyi wata tafiya daban , kamar ziyarar ƴan uwa , to anan ba za suyi aiki da hukuncin da suke aiki dashi ba a lokacin da suke gudanar da sana'arsu ba , suma za su ɗauki kansu kamar sauran mutane ne a wannan hali na tafiya .


9/Ramdan/1444H - 21/3/2023

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post