Sayyidina Ali Ibn Abi Talib (AS) A Yakin Khandak (Yakin Gwalalo) !!!

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Karfin da Musulunci ya yi ya sanya Yahu*dawa suka ji cewa karfin Manzon Allah (SAW) babbar Barazana ne gare su, don haka sai suka shiga yin makirce-makirce ga da'awar Musulunci da Annabinsa, inda suka shiga jan hankulan makiya Musulunci don samar da wata babbar Rundunar taron dangi don Afkawa Madina da gamawa da Musulunci Baki dayansa.


Sai suka tuntubi kabilun Kuraishawa da Gabaɗayansu, suka dace da su a kan kai wa Madina hari da Rushe da'awar Musulunci, sai dai labarin haka ya isa kunnen Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallama don haka sai ya shawarci Sahabbansa kan yadda za'a bullo wa lamarin. Sai Salman al-Farisi (RA), Wanda ke cikin manyan Sahabbansa, ya ba shi shawarar da su kewaye Madina da rami, (Gwalalo) sai Manzo ya karbi wannan shawara, ya shiga haka rami tare da sauran Musulmi.


A Bangare Daya kuma Kuraishawa sun yi tanaji da kuma tara Dakarunsu, masu taimaka musu da sauran mabiyansu, ta yadda adadin rundunarsu ya kai mayaka dubu goma, (10.000) suka kama hanyar Madina.


Shi kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai ya shirya Sahabbansa don Yaki, Adadinsu ya kai mayaka Dubu uku.


Harin makiya ya fara yayin da Amru bin Abd Wudd al-Amiri ya ketare Ramin, ya shiga yin barazana ga Musulmi yana kira da cewa: "Ko akwai mai fito-na-fito da ni?" Sai Ali bin Abi Talib (AS) ya mike ya ce: "Ni ne zanje gare shi ya Manzon Allah". Sai Manzo (SAW) ya ce: "zauna Amru ne fa!?


Sai Amru bin Abdu Wudd ya maimaita kiransa, ya shiga yi wa Musulmi izgili. Sai Ali (AS) ya Sake mike ya ce: "Bar ni da shi Manzon Allah". Sai Annabi ya kara cewa: "zauna Amru ne". Sai Ali (AS) ya ce: "Ko da Amru ne kuwa" Sai Manzo (SAW) ya yiwa Sayyadina Ali izini ya ba shi takobinsa Zul-fikari, ya sanya masa garkuwarsa ya kuma nada masa rawaninsa, sannan Manzo ya ce:


A fahimci cewa wannan jaddadawa da Manzon Allah (SAW) ya ke na cewa "Zauna Amru ne fa" ba don saboda yana yi ne don yana kokwanto Imam Ali (AS) zai gaza ba ne wajen ka*she Amru, face dai yana yi ne don ya nuna wasu abubuwa: 


Na farko dai ya nuna matsayin Imam Ali (AS) na jaruntaka, na biyu kuma kana mafi muhimmanci yana so ne ya jarraba sahabbansa ya gani ko wani zai taso ya fuskanci Amru ko kuma suna Shakkarsa saboda sanin irin jaruntakar da Amru din yake da ita. 


To hakan kuwa ya faru don kuwa babu guda daga cikin sahabbai da ya nuna Alamar mikewa da fuskantar Amru.


Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yayi addu'a Yace:


"Ya Allah wannan dan'uwana ne kuma dan baffana ya Allah kar Ka bar ni makadaici don Kai ne mafi alherin Mai gadarwa.


Sai Ali ya gabata da kwazon nan na shi da ya saba, sai ya kara da Amru karawa mai tsanani, daga karshe dai ya bar shi kwance mata*cce.


Sai Musulmi suka yi kabbara yayin da suka ga Amru kwance a kasa kuma Ali na dawowa da nasara, sai Manzo (SAW) ya tarbe shi da fadarsa cewa:


"Saran da Ali ya yiwa Amru bin Abd Wudd tafi ayyukan al'ummata har Ranar kiyama.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post