Wafatin Sayyid Abdul Hussain Sharafuddin...!!!


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


A rana mai kamar yau 8 ga watan Jumadha Thaniya , shekara ta 1377 , Wannan Babban Malami mai girma da daraja yayi wafati , wato Sheikh Abdul Hussain Sharafuddin Almusawi .


TAKAITACCEN TARIHINSA 


An haifeshi ne a garin Kazimiyyar Iraqi a shekarar 1290 Hijriyya ,a lokacin Daular Usmaniyyawa ya kuma rasu a garin Sur na ƙasar Lebanon , an kawoshi garin Bagdad daga nan kuma aka rako Jana'izarsa har zuwa Najaf mai Alfarma, sannan aka binne shi a kusa Ƙabarin Imam Ali (a.s) .


Sayyid Abdul Hussein na ɗaya daga cikin Jagororin farfado da kasar Labanon da suka samu 'yancin kai. Ya bayar da fatawa a kan yaƙar Turawan mulkin mallaka na Faransa, kuma wannan fatawar ta sa ya bar ƙasar Labanon a lokacin da sojojin Faransa na mulkin mallaka suka kai wa kauyensa hari, amma ya dawo bayan hijirar shekara guda da yayi .


Yayi manyan Ayyuka daban-daban dan cigaban Addinin Musulunci  , mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne Littafin Almuraja'aat (المراجعات) , wanda Asalinsa wasu tarin wasiƙu ne da suka gudana tsakaninsa da Sheikh Salim Al-Bishri, Babban Shehin Azhar a zamaninsa, da kuma Littafin Nassi da Ijtihadi (النص والإجتهاد ) , wanda ya rubuta a ƙarshen shekarun rayuwarsa, kuma an fassara su zuwa harsuna daban-daban na duniya .

Kuma suna da matuƙar Muhimmanci mutum ya karantasu , musamman me neman gaskiya game da abinda ya shafi Shi'anci.


Haka nan yana ɗaya daga cikin waɗanda suka fara yaƙi da hijirar Yahudawa zuwa Palastinu, kuma ya yi imanin cewa hijirar Yahudawa zuwa cikinta barazana ce ga makomar Falasdinu, kuma dole ne a tashi tsaye wajen ganin bayan wannan turawan mulkin mallaka.


Har wa yau yana daya daga cikin Malaman da suka shahara wajen ƙoƙarin samar da Kusanci tsakanin ɓangarorin Musulunci da yin Wahda, ya kuma yi ƙokarin warware wasu manya-manyan sabanin dake tsakanin Shi'a da Ahlussunna Wal jama'a, shi yasa yake da Tattauanawa da Munazarori tsakaininsa dasu dayawa , A Misra da Saudiyya har yana da tattaunawar da yasa Sarkin Saudiyya Abdul Aziz Aali Sa'ud ya yarda da halascin Tawassuli da Neman Albarkar Annabi (saww) da Iyalansa tsarkaka.


Yayi karatu a birnin Samarra da Najaf mai Alfarma a hannun manya manyan Malaman zamaninsa Kamar Mirza Hussein Nuuri , Al-Akhundul Khurasani  dama Wasunsu ,Allah yayi musu Rahma baki ɗaya .


✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post