Wacce Nana Fiddah Yar Garin Naubah(S'a)????



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 


GUYANGAR SAYYIDAH ZAHRAH (S. A) MAI MAGANA DA ALQUR'ANI 


Shi dai yankin Naubah dake Afrika yanki ne dake gabas da kogin Nilo tsakanin Aswan da Dinkalah a (Sudan). Yankin Naubah bangare biyu ne, wato akwai Naubah ta gangare da Naubah ta tudu. 


Naubah ta gangare ita ce yankin dake tsakanin Masar da Sudan, da kuma kwarin Hulafa'a. 


Ita kuma Naubah ta tudu ita ce yankin dake Sudan. Muslimci ya shigo gun ne a qarnin farko na Hijrar Annabi (S. A. W. W) .


Su dau Naubawa sun shahara da kyawawan dabi'u ko siffofi ababen yabo, wanda ke nuna suna da sauran kyawawan al'adu wadanda aka halacci mutane a kanta. 


Daga cikin kyawawan dabi'unsu sun hada da :


Zaman lafiya, 


Wadatuwa da kadan, 


Jaruntaka da taimako, 


Girmama al'adun wasu jama'a da gargajiyarsu da kuma, 


Riqon amana da yin aiki bisa Ikhlasi .


Ya zo cikin cikin littafin Al-Isabah na Ibn Hajar Al-Asqalani ya ambato cewa an riwaito daga Imam Sadiq daga iyayensa daga Aliyu (A. S) cewa Manzon Allah (S. A. W. W) ya bawa 'yarsa Fatima mai aiki sunanta Fiddah 'yar garin Naubah don ta riqa taimaka mata da aiki. Kuma ya sanar da ita wata addu'ah wacce take yin addu'ah da ita. Sai wata rana Fatimah tace mata kullum za ta riqa yi musu waina (Masa). Sai tace a'a, za ta riqa kwaba qulli kuma ta riqa yiwo mata Itace.


Wata rana Nana Fiddah ta tafi yiwo Itace, bayan ta gama yayin da tazo dauka sai ta kasa, sai tayi wannan addu'ah wacce Annabi (S. A. W. W) ya koya mata. Ga ta kamar haka :


" YAA MAKADAICI WANDA BABU WANI KAMARSA. KANA IYA KASHE KOWA KUMA KANA BISA AL-ARSHINKA MADAIDAICI. GYANGYADI BA YA KAMA SHI BALLE BACCI. "


Sai ga wani Balaraben Qauye yazo ya dauki wannan damin Itacen ya kai mata har zuwa qofar gidan Sayyidah Fatimah (S. A). 


YADDA TAKE MAGANA DA ALQUR'ANI 


Don jin yadda take magana da Al-Qur'ani sai ku biyo mu kamar haka :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


أَبُو الْقَاسِمِ الْقُشَيْرِيُّ فِي كِتَابِهِ قَالَ بَعْضُهُمْ‏ انْقَطَعْتُ فِي الْبَادِيَةِ عَنِ الْقَافِلَةِ فَوَجَدْتُ امْرَأَةً فَقُلْتُ لَهَا مَنْ أَنْتِ ?


Abu Qasim Al-Qushairiy ya kawo cikin littafinsa cewa, sashensu yace : " Mun tafi cikin wani Qauye cikin wani Ayari sai muka sami wata mata, sai nace mata, ke wacece ?


 فَقَالَتْ : " وَ قُلْ سَلَامٌ فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ‏."


Tace : " KACE SALAMUN, DA SANNU ZA KA SANI (wato ka fara da sallama). "


 فَسَلَّمْتُ عَلَيْهَا فَقُلْتُ 

مَا تَصْنَعِينَ هَاهُنَا ?


Sai nayi mata sallama kuma nace, me kike yi anan ?


 قَالَتْ‏: " مَنْ يَهْدِ اللَّهُ‏ فَلَا مُضِلَّ لَهُ‏."


Tace : " AI DUK WANDA ALLAH YA SHIRYAR BABU MAI 'BATAR DASHI. "


 فَقُلْتُ: أَ مِنَ الْجِنِّ أَنْتِ أَمْ مِنَ الْإِنْسِ ?


Sai nace : Ke kuwa daga Aljannu kike ko kuma daga cikin mutane 


 قَالَتْ‏: " يا بَنِي آدَمَ خُذُوا زِينَتَكُمْ‏"


Sai tace : " YAA KU 'YAN ADAM KU RIQI ADONKU (ma'ana kayi abinda ke gabanka kawai). "


 فَقُلْتُ: مِنْ أَيْنَ‏

أَقْبَلْتِ ?


Sai nace, " TO, DAGA INA KIKA FITO ? "


قَالَتْ‏: " يُنادَوْنَ مِنْ مَكانٍ بَعِيدٍ. "


Tace: " SUNA KIRA DAGA GURI MAI NISA (gurin dana fito yana da nisa). "


 فَقُلْتُ: أَيْنَ تَقْصِدِينَ ?


Nace, yanzu kuma ina kika nufa ?


 قَالَتْ‏: " وَ لِلَّهِ عَلَى النَّاسِ حِجُّ الْبَيْتِ‏. "


Tace : " AN WAJABTAWA MUTANE HAJJI (ma'ana dole na koma inda na fito). "


 فَقُلْتُ : مَتَى انْقَطَعْتِ?


Sai nace, yaushe kike wannan guri (bayan kika kasa komawa inda kika fito) ?


 قَالَتْ‏ : " وَ لَقَدْ خَلَقْنَا السَّماواتِ وَ الْأَرْضَ‏ ...

فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ‏ "


Sai tace : " HAQIQA ALLAH YA HALICCI SAMMAI DA QASSAI .......CIKIN KWANA SHIDA. "


فَقُلْتُ: أَ تَشْتَهِينَ طَعَاماً ?


Sai nace, kina sha'awar abinci ? 


فَقَالَتْ‏ : "وَ ما جَعَلْناهُمْ جَسَداً لا يَأْكُلُونَ الطَّعامَ‏ "


Tace : " AI BAMU SANYA SU JIKI (kamar Mala'iku) BA SA CIN ABINCI BA. "


فَأَطَعَمْتُهَا ثُمَّ قُلْتُ هَرْوِلِي وَ لَا تَعَجَّلِي.


Sai na ciyar da ita sannan nace, kiyi a hankali kada kiyi gaggawa. 


 قَالَتْ‏: " لا يُكَلِّفُ اللَّهُ نَفْساً إِلَّا وُسْعَها "


Tace : " ALLAH BA YA 'DORAWA RAI (wani abu) FACE IYAWARTA. "


فَقُلْتُ: أُرْدِفُكِ?


Sai nace, nayi miki rakiya (wato na dauke ki kan abin hawana na raka ki) ?


 فَقَالَتْ‏: " لَوْ كانَ فِيهِما آلِهَةٌ إِلَّا اللَّهُ لَفَسَدَتا."


Sai yace : " DA DAI CIKINSU (sammai da qassai) AKWAI WANI ABIN BAUTA (wanda ba Allah ba) DA SUN RUGUJE. " (Ma'ana kasancewa mutum biyu wadanda ba Muharramai ba akan abin hawa na da matsala). 


 فَنَزَلْتُ فَأَرْكَبْتُهَا

 

Sai na sauka (daga kan abin hawan nawa) ita ta hau. 


 فَقَالَتْ‏: " سُبْحانَ الَّذِي سَخَّرَ لَنا هذا "


Sai tace : " TSARKI YA TABBATA GA (Allah) WANDA YA HORE MANA WANNAN (abin hawa mai sauqaqa mana wajen tafiya da daukar kaya). "


فَلَمَّا أَدْرَكْنَا الْقَافِلَةَ قُلْتُ أَ لَكِ أَحَدٌ فِيهَا?



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post