TUNATARWA GARAYUWAR MUTAYAZU

 



(1)- Kasantuwar ku ‘yan gwagwarmaya abu ne mafi muhimmanci ka gyara kanka, kuma wajibi ne ka gyara tsakanin ka da Allah mai rahama.


(2)- Wajibi ne gareku ku mutunta junanku tare da sanya soyayya a tsakanin ku, da gujewa cece-kuce.


(3)- Dole ne idan ka kasance ɗan gwagwarmaya ka kare mutuncin sister's ɗin harka islamiyya koda hakan zai zama jinin ka za'a zubar dashi ne, domin Sayyid yayi mana umarnin kare mutuncin matan mu.


(4)- Lazim ne ka siffantu da kyakkyawan ɗabi'u na karamci da girma, da kuma ƙoƙarin banbanta da sauran mutanen gari.


(5)- Wajibi ne ka kiyaye yaudarar macen data aminta da kai a matsayin zaɓin rayuwar ta, da kuma ƙoƙarin tunatarwa gareta game da sanya hijabi ko wani lokaci.


(6)- Karki kasance mai yawan bin ƙawayen da basu kamata ba, kama daga;

- school

- Anguwa

- da kuma makwabtaka.


(7)- Dole ki fita daban da sauran matan da kike tare da su, domin kare mutuncin ki da kuma ƙoƙarin su fahimci kiran jagoran ki.


(8)- Compulsory ne ya zama madubin ki jagoran kine a kullum.


(9)- Dole mu zama masu taimakawa junan mu tare da sauke dukkan nauyin daya hau kawukanmu.


(10)- Wajibi ne biyan hakkin Shuhada domin wata rana kai ma wannan mu'assasar idan Allah ya baka shahada zasu temaki iyalanka.



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post