Tarishin Sayyada Fatima Zahara(A's)


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 


Daga Comr Abdulmumeen Salisu

Youngest Activist

08035949883


GABATARWA 

Manzon Allah (s) ya kasance yana yiwa Sayyida Zahra (as) lakabi da "Shugabar Matan Talikai" kuma ya yi mata alkunya da "Babar Babanta" yana son ta so mai tsanani, kuma yana girmama ta girmamawa mai girma, har ya kasance idan ta shiga wajansa sai ya yi maraba da ita ya mike tsaye domin girmama wa gareta, sannan kuma ya zaunar da ita wurinsa, wani lokaci har ya sumbanci hannunta, kuma ya kasance yana cewa: Allah yana yarda da yardar Fadima yana kuma fushi da fushinta.

Wannan diya ma’abociyar girma da daukaka, wacce Allah ya so ya zabeta ya sanyata ta zama shugaban dukkan matayen talikai baki dayansu duniya da lahira, wato Sayyida Fatima Azzahara (AS), wacce Allah ya sanya ta ta zama tsokar jikin Mahaifinta.

Sananne abu ne cewa Fatima (as) it ace fiyayyiyar dukkan matayen talikai na zamanininta da na gabanin hakan. Kai! Ita ce fiyayyiya akan dukkanin wata halitta da Allah (T) ya yi ta a matsayin jinsin mace.


Kana iya tabbatar da wannan kuwa, idan ka koma ga wasu ruwayoyi da suke bayani sanka-sanka akan hakan a cikin littafin “Al-Kisal” shafi na 205. A babin da yake bayani akan shugabannin matayen Aljanna guda hudu ne, kuma Sayyida Fatima ‘Yar Manzon Allah Muhammad (S) ita ce fiyayyiyarsu.

In kana bukatar sanin ko wace ce wannan baiwar Allah mai girman daraja, dole ne ka ziyarci littattafan magabata ka karanta ruwayoyin hadisai da aka ruwaito dangane da girma da daraja da fifiko da isan wannan tsarkakakkiyar Uwa, ma’abociyar girma da matsayi da daukaka gami da fifiko matabbaci.


SAMUWAR SAYYIDA ZAHRA (AS)

Sayyida Zahra (as) an haifeta ne a dai dai lokacin da duniya ta dauki mata a matsayin kaskantattu, inda wasu ma binnesu da rai ake, har yakan zama abin kunya ga mutumin da yabar 'ya mace a gidansa bai binne ta ba.

Bayan auren Nana Khadija (as), Allah ya jarabci Manzon Allah (S) da rasuwar 'ya'yansa wanda suka kasance duk maza ne, har kafiran larabawa suna yi masa gorin bashi da magaji, har suke kiransa da "Abtar" ma'ana mai yankakken baya. Sukace "ku kyaleshi ai bashi da wanda zai gajeshi in ya mutu shikenan addininsa (Addinin musulunci) shima ya mutu sun huta", Sai Allah ya saukar da Suratul Kauthar domin rarrashin Manzon Allah (S) daga gorin da kafirai sukayi masa.

Wasu malamai sunce a'a Kauthar wata koramace a aljanna ba Sayyida Zahra (as) ake nufi ba, amma mafi yawan malamai sun tabbatar da cewa tabbas sayyida Zahra (as) ake nufi da alkauthar.


An ruwaito a cikin littafin “As-Siradal Mustaqeem, Juzu’I na 1, shafi na 170, fasali na 5”, daga Annabi Muhammad (S) yana cewa: “Lokacin da akai Isra’I da Ni, na shiga Aljanna, sai Mala’ika Jibril (AS) ya kawo min ‘Tuffah’ (Apple) na ci, sai ya narke ya zama Maniyi, FATIMA daga wannan (tuffah) din take. Duk lokacin da nai shaukin shakan kamshin Aljanna, nakan fuskanci Fatima (na shaki kamshin daga gareta).”

A cikin wani hadisin kuma daga Annabi (S) ya ce: “Ku sani wannan ‘tuffah (apple) din Allah (T) da kansa ne ya halicce shi, sannan ya mallaka shi ga Annabinsa a yayin Mi’iraji.” – Tawilul Ayat; 241.

Kaga ita Sayyida Azzahara (SA) an samar da maniyinta ne daga abincin Aljanna. Kuma wani Karin falala ma, sai ya zama Allah (T) da kansa ne ya samar da wannan sinadarin da ya tarce kan cewa ta hanyar sa ne za’a samar da wanann tauraruwa mai albarka.


HAIHUWAR SAYYIDA ZAHRA (AS)

Ya zo a cikin littafin Dala'ilul Imama na Muhammad Ibn Jarir Addabari Asshi'i shafi na 15 Abu Basir ya rawaito daga Imam Sadik (as) ya ce: "An hafi Sayyida Fadima a watan Jumada akhir ran ashirin daga cikinsa, shekara arba'in da biyar bayan haifar Annabi (saww)". Kunga kenan an haifi Sayyida Zahra (as) shekara biyar bayan aiko Annabi (saww) duk da cewa akwai ruwayoyi mabanbanta amma wannan shi ne zance mafi shahara kuma mafi karfi.

A lokacin da Nana Khadija nakuda ya taso mata, ta aikawa matan kuraishu domin suzo su taimaka mata irin taimakon da mata kewa junansu yayin haihuwa, amma suka ki amsa mata, kwatsam sai ga yan sako daga Ubangijin al'arshi ya turo domin a taimaka mata, daga ganinsu sai ta tsorata sai sukace mata karta tsorata ko bakin ciki. Tsarkakakkun mata ne suka karbi haihuwarta, waenda suka karbi haihuwar sayyida Zahra (as) sune; Maryam bint Imran (Mahaifiyar Annabi Isa), Hasiya bint Muzahim (Matar fir'auna), Ummu khulsum ('yar uwar Annabi Musa) sai Saratu (Matar Annabi Ibrahim), daya ta zauna gabanta daya kuma a bayanta daya a hagunta daya kuma a damanta, a haka Sayyida Zahra ta sauko duniya tana mai Sujada da godiya ga Allah (S), tayi kalmar shahada sannan ta kalli matayen nan tayi musu gaisuwa irin ta addinin musulunci sannan ta kirayi sunayensu daya bayan daya (daga saukowarta duniya).


TASOWA DA AUREN SAYYIDA ZAHRA.

Sayyida Zahra (sa) tun tasowar ta baiwar Allah ce mai yawan ibada, mai tausayi ce, mai hakuri gata da kyauta, tana da kyawawan dabi’u abin koyi, saboda irin kyawawan dabi’unta babu yadda za’ayi kayi mu’amala da ita ko ta sakan daya ce baka kwaikwayi.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post