Tarihin Dr. Abduljabbar Shaikh Nasiru Kabara.....!!!


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 


Tabbas Tarihin Dr.Abduljabbar kabara duk Wanda Yasanshi Yasanshi ne akan Tattauna Mas'aloli da Bahasi Tsakanin Izala da Ɗarika a Kano da ƙasa baki ɗaya. 


Dr. Abduljabbar ɗan Darikar Qadiriyyah ne wadda Hedikwatarta ke Kano, kamar yadda Kano tana cikin Hedikwatocin Dukkan ɓangarorin ƙungiyoyin addinin Musulunci a Nigeria.  


Abduljabbar ya taso ne a cikin zafin rikicin martanoni tsakanin malaman Ɗarika da takwarorinsu na Izala ɓangaren Salafiyyah da wahabiyya. 


Lokaci guda manyan malaman kano ɓangaren ɗariƙa suka ga basu da wani zaƙaƙuri mai ilimi da bincike wanda karfinsa yakai akan yayi bahasi da tankawa kowanne malami na ɓangaren izala sai Mallam Abduljabbar...


Hakan yasa dukkan Malaman Ɗariƙa suka Tsaya akan Cewa Dr.Abduljabbar Garkuwarsune...  


Duk da cewa Dr.Abduljabbar ya tattauna mas'aloli da dama, yayi rubututtuka da dama waɗanda har yanzu ba'a samu wani malami wanda ya iya biyo hanyar da Dr.Abduljabbar ya biyoba wajen yin raddi..


Bayan Jajircewa da Tsayuwar Dr.Abduljabbar kabara malaman ɗariƙa sun sami sukuni a ƙasar hausa bayan Tsangwama da zagi da ƙiyayya da malaman izala suka cusawa Al'ummar ƙasar hausa gameda malaman ɗariƙa... 


Tabbas Dr.Abduljabbar ya samu dama ya leƙa wasu rubuce-rubuce na mulhidai da zindiƙai daga cikin musulmi da kuma mustashrikun na malaman kiristoci, waɗanda suke aibata Manzon Allah (S.A.W) da Sahabbansa, suke yiwa hadisai mummunar fassara domin su yi zagi ga janibin Annabi (S.A.W) Binciken Dr.Abduljabbar kuwa ya ƙara ƙarfafarsa akan Banbance ƙarya da gaskiya gameda hadisan da ake jinginawa Annabi S.A.W


D.rAbduljabbar ya cigaba da kutsa kansa a cikin manhaji na soke hadisan ƙarya da aka jinginawa Manzon Rahama S.A.W Babbar manufarsa ita ce rusa ruɓaɓɓun Hadisan da aka Cusa Cikin Bukhari da Muslim da sauran littafan hadisi.


Binciken da Dr.Abduljabbar ya aiwatar ya tabbatar da cewa anyi cushe wajen ƙirƙirawa Annabi (S.A.W) ƙarya domin rusa Addini Bayan Wafatin Annabi duk wani malami ya tabbatar da hakan, saidai son zuciya da ƙiyayya da ƙullaci da suke yiwa Dr.Abduljabbar... 


Dr.Abduljabbar yayi aiki tuƙuru wajen fito da maruwaita waɗanda suka samu zamewar harshe da alƙalami wajen rubuta munanan hadisai da ingantasu, suka ƙirƙirawa Annabi (S.A.W) amman malamai suka ci gaba da ɓoye hakan tsawon shekaru fiye da dubu ! Wannan kai tsaye shine matsayin Dr.Abduljabbar.. 


Bayan Dr.Abduljabbar ya gama bincikensa tsaf ya dinga ɗauko maganganun malaman shi'ah da na sunnah yana haɗawa, ya tabbatar da cewa malaman shi'a suna da gaskiya a cikin dukkan wata mas'ala da aka saɓa dasu 75%... 


Zindiƙai mulhidai da malaman kiristoci sun samu nasara akan musulmai ta dalilin rashin haɗin kansu...  


Dukkan abubuwan da Dr.Abduljabbar ya faɗi karantosu ya yi kuma Akwai su a wurare da dama kamar yadda ya ke faɗa, waɗanda suke nuna cewa Marawaita da wasu daga mazauna fadar Annabi sun samu tuntuɓen harshe da alƙalami, sun shigo da wani abu cikin shari'ah wanda ba zai yiwu a ce daga Annabi (S.A.W) ne ba (wannan shine malamai suke kira da sukar hadisi ta ilimin "Dirayah" , wato ilimin fahimtar ko abinda hadisi ya ke karantarwa ya yi daidai da shari'ah ko bai yi ba , a maimakon sukar hadisi da ilimin "riwayah" , wato la'akari da ingancin isnadi, Dr.Abduljabbar duka biyu din ya ke amfani da su , sai dai ya saba wa malamai da suka ce ba a sukar hadisi da Sahabin da ya ruwaitoshi , saboda Sahabbai dukkansu adilai ne.


Cikin Rigimar Tsaftace hadisai Dr.Abduljabbar a mafi yawan Lokaci yana cewa shi bai aibata annabi ba malaman hadisi da marawaita sune suka aibata annabi, Wannan ya jawo mafiya yawa daga ɓangarorin malaman Kano, waɗanda suke karɓar sunan "Ahlussunnah" ko da kuwa da "faffadar ma'anar" kalmar ne, suka yi maja domin yaƙar Dr.Abduljabbar saboda ra'ayinsu na ganin sun durƙusar dashi da son zuciyarsu ba don abunda suke faɗa ya aikata ba.


Malaman "Maja" sun yi nasara a kan tilastawa gwamnatin Kano ta labtar da Dr.Abduljabbar.  


Da yawa daga malaman maja suna cewa Dr.Abduljabbar ya zama ɗan shi'a, kuma yana yaɗa aƙidun shi'ah a cikin rigar Sunnah, don kawai ya samu nasara a kan 'yan Izala..


FITOWA TA FARKO

Naziru Yakubu Umar Abaya

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post