Shin Yan Shi'ah Basu San Sayyiduna Ali(A's) Yana Da Da Mai Suna Abubakar Da Umar Da Kuma Usman Bane???




[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 


Sukance mana : Ƴan Shi'a sunce an samu saɓani da rikici tsakanin Sahabbai har ta kai ga anyi yaki da kashe-kashe , ya isa mu kore rashin saɓani da jituwa a tsakanin Imam Ali da Khulafa'u , sanyawa ƴaƴansa suna Abubakar, Umar da Usman , shin wannan baya nuna Ƙauna da kusanci da kyakkyawar fahimta a tsakaninsu ? Da akwai sabani da Imam Ali bai sawa ƴaƴansa wadannan sunaye ba ! Me za kuce game da hakan Ƴan Shi'a???


AMSA 


Dangane da wannan Shubhar za mu iya bada amsa ta fuskoki daban daban daga cikin amsar da za mu basu shine : 


1 . Babu wani dalili da ya tabbatar da cewa wai Imam Ali (a.s) ya sanyawa Ɗansa suna Abubakar yana nufin Abubakar Bin Abi Ƙuhafata , Ko Umar yana nufin Umar ɗan Khaɗɗab , ko yasa Usman yana nufin Usman bin Affan , In akwai dalili akan haka muna ƙalu balantarku ku kawo mana shi a tashin farko , bari ma dai akasin hakan ne ya tabbata kamar yadda za mu kawo dalla-dalla a gaɓoɓi masu zuwa .


2 . Tabbas Imam Ali yana da wani ɗa dake kiransa Abubakar, to amma kuma ya kamata susan Abubakar ba Suna bane Alkunya ce , duk wanda yasan larabci yasan duk Sunan da ya fara da "Abu" to Alkunyace ba asalin sunan bane , Alkunyar Annabi Abul Ƙasim shiko Imam Ali Abul Hassan ... don haka Shi Abubakar Ɗan Imam Ali (a.s.) Sunansa na gaskiya shine Muhammadul Asgar , saboda Imam Ali yana da Ƴaƴa biyu masu suna Muhammadu (Muhammad Binil Hanafiyya da Muhammadul Asgar) , dan a banbancesu ake kiran ɗaya Muhammad Binil Hanafiyya ƙaramin kuma ake kiransa Asgar (Ƙarami) Alkunyarsa kuma Abubakar .

Kuma Alkunyar Abubakar ta shahara a wajen Larabawa a wancen lokacin , yanzu ne mu Hausawa muke ɗaukarsa a matsayin sunan yanka , don haka sunan Ɗan Imam Ali (a.s.) Muhammad , Laƙabinsa Al-asgar , Alkunyarsa kuma Abubakar , ba wai Abubakar Bin Ƙuhafa ba .


2 . Dangane da ɗan Imam Ali (a.s.) mai suna Umar , ya kamata kusan an samu saɓabi wajen Dhabɗin (Ainihin furucin sunansa ) , domin kuwa har a wajen Malaman Hadisinku cikin Asaanidu kamar Tirmizi sunyi Dabɗinsa da Amru (عمرو)ba Umar (عمر) ba , saboda a rubuce da Amru da Umar babu banbanci daga baya ne ake ƙara harafin Wawun dan a banbancesu amma da ba'a banbancesu sai a Lafazi , duk wanda ya karanta Ilmin Rasmin Larabci yasan hakan .


To a ɗauka ma sunansa Umar ba Amru ba , hakan baya nuna Imam Ali (a.s.) yasa masa sunan Umar Bin Khaɗɗab ne , domin kuwa a Sahabban Annabi (saww) akwai masu suna Umar kamar Umar bin Abi Salamata , kenan zai yu ɗayansu ake nufi ba sai Ibnu Khaɗɗab ba ? Malamai suna cewa (إذا ورد الإحتمال بطل الإستدلال ) , ma'ana in shakku da tantama suka shiga cikin dalili to kafa hujja dashi ta ɓaci , don haka ba wani dalili da zai tabbatar da Umar Bin Khaɗɗab Imam Ali (a.s.) yake nufi da sunan ɗansa in kuma akwai a kawo mu gani .


3 . Sunan Umar abune daya yaɗu a wajen Larabawa domin yana daga sunaye mafiya shahara a lokacin , to Menene dan Imam Ali (a.s) ya sanyawa ɗansa wannan sunan a matsayinsa na Balarabe dayake rayuwa a cikin larabawa.

Ballantana ma Alhamdulillahi sunansa Amru , wanda asalin sunan kakan Imam Ali (a.s.) ne kuma kakan Manzon Allah (saww) wanda muka fi saninsa da Hasim , kamar yanda zan tabbatar da haka a gaɓa ta 8 mai zuwa .


4 . Usman ɗan Imam Ali (a .s) kuwa ai lamarin sunansa a bayyane yake , domin an tambayi Imam Ali (a.s.) me yasa ya sakawa ɗansa suna Usman Shin yana nufin Usman Bin Affan ne ? Sai ya bada amsa da cewa ;

إنما سميته باسم اخي عثمان بن مظعون .....

Ma'ana : Kaɗai dai na sanya masa sunan ɗan uwana Usman Bin Maz'uun. 


Sunan wani Sahabi ne daga cikin Sahabban Annabi (saww) wanda shine farkon wanda aka fara binnewa a Maƙabartar Baki'a , kuma shine farkon wanda ya fara rasuwa daga cikin Sahabbai Muhajiruna a garin Madina .


-Abul Faraj ya kawo hakan aa cikin littafinsa مقاتل الطالبيين shafi na 85 . 


5 . Abinda yake mafi Muhimmanci ya kamata susan cewa :

Saka suna baya nuna munasaba da alaƙa a tsakanin sunaye sai in dalili ya tabbatar da hakan , abune da yake sananne cewa mafi yawan sunayen yanka ana sakasu ba tare da munasaba ba , wani ya saka sunan ne ba dan mai Asalin sunan ba sai dan sunan yana birgeshi ko ma'anarsa mai kyau ce , wani yasa ne saboda sunan ya shahara a tsakanin Mutane...... Ko wani ma saboda gado aka saka masa sunan kakansa ne kamar sunana Misali , hakan shima dan Imam Ali (a.s.) "Amru"sunan kakansa ne ba wani ba .


6 . Uwa uba kuma shine in saka sunan da Imam Ali (a.s) yayi na nufin soyayya da ƙauna da kyakkyawar fahimta , me yasa su Sahabban nan Uku da ake magana akansu , bamuga sun sakawa ƴaƴansu sunan ƴaƴayen Imam Alin ba ? Kamar Hassan Hussain ko su saka mai suna Alin kansa , kenan basa son Imam Alin ne shi yasa basu sakawa ƴaƴansu sunan Ali ba ! Indai har suna shi ke nuna so da kyakkyawar fahimta da Jituwa a tsakani .



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post