Saura Kwanaki 11 A daina Karbar Tsofaffin Kudade Me Ya Kamata Kayi???


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Tun bayan sanarwar babban bankin kasa CBN game da canja takardar kudi kama daga N200, N500, da kuma N1,000 'yan Nigeria suke faman jiran yadda lamarin da ake kira Naira redesign zai kasance.


Haka nan a ranar 15 December 2022 a ka sake sabbin kudaden, inda a yanzu suke yawo a Nigeria duk da sun yi karanci.


A matsayinka na dan kasuwa me ya kamata ka yi?


1. Ka yi kokari ka je banki ka canja kudadenka nan da mako daya


2. Daga ranar da aka haramta karbar tsohon kudi wato 31st January 2023 to kai ma kada ka karba


3. Duk da karancin da sabbin kudaden suke yi, kada ka yi kokarin karya dokar CBN na kin kai kudadenka banki


4. Idan aikinka shi ne hada-hadar kudi kuma aikin POS kada ka bari a tara maka tsoffin kudade daga 26 January 2023


5. Idan ba ka samu sabon kudi ba kuma kana da tsoffin kudi da yawa, ka yi kokari ka batar da su ko kuma cikin sauki ka kai su banki, amma dai duk rintsi kar ka bar su a gida


Fatan alheri


—Muhammad Auwal Ahmad (#Mohiddeen)

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post