Ranar Yaumu Zahara Yaya ’Yan’uwa “Sisters” Ya Kamata Su Kasance?

 



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 



—Daga: Ibrahim Y. Ibrahim


Sayyada Zahara (s.a) ita ce shugaban matan duniya baki ɗaya‚ Itace ƙwara ɗaya rak ma’asuma Kammalallan (Isma) daga cikin mata, tun daga kan Hauwa’u har zuwa kan wanda za’ayi hurin ƙaho a kansu. Sayyada Zahara (s.a) itace ƙwara ɗaya rak ya zama cewa da ba Imam Ali (a.s) da Sayyada Zahara bata samu mijin aure ba‚ babu dai-dai da ita wanda ya kamata ya zama mijin ta.


Duba da matsayi da girma irin na wannan baiwar Allah ’Ya a gurin Manzon Allah (S.a.w.w) ya zama cewa sonta wajibi ne ga ko wane musulmi. Kasancewar haka Almajiran Sheikh Zakzaky (H) suna bukukuwa da walima na Mauludin Sayyada Zahara (s.a) domin nuna Soyayyar su gareta. Ana kiran wannan ranar ranar mata na duniya a musulunci kasancewar itace shugaban matan duniya da lahira.


Wace hanya ce ’Yar’uwa maya zata nuna Soyayyar su ga Sayyada Zahara? Yaya ya Kamata ’Yar’uwa mata su kasance a wajan Mauludin Sayyada Zahara (s.a)? Sayyada Zahara zata Amshi Soyayyar kine wajan koyi da ɗabi’unta da irin shigan da yadda ta zauna da imam Ali (a.s), ki sani Sayyada Zahara baza tayi farin ciki kina cewa kina sonta a gan-gan jiki amma bakya koyi da ɗabi’unta wajan kiyaye dokokin ubangiji Allah ta'ala.


A naki tunanin zaki wajan taron “YAUMU ZAHRA” amma ki caccaɓa kwalliya a fuskar ki da sanya Hijabi wanda zai ɗauki hankalin da sanya turare mai ƙamshi da kin gifta za’aji? Yan’uwa mata Hijabin ku ya zama yana da faɗin da mutum baze gane ya jikinku yake ba, baza a gane ya ƙirjinku yake ba, da sauran siffar jikinku‚ da sauran siffar da Allah ta'ala yayi ma mace na ado.


Ya zama cewa: kunsa lulluɓi me faɗin da baze nuna‚ wanda ke ganin ku baze san yaya jikin ku yake ba‚ ya ‘Shape’ ɗin jikinku yake? Baze sani ba.To in kayi haka Shine kasa Hijabi ki tsaya ki nazu wajan sauraren gwala-gwalan jawabai ranar yaumu Zahara. Sayyada Zahara za tayi farin ciki da yardar Allah.


Allah ya tausaya mana, ya yafe gazawar mu, ya ƙarfafafi ɗan ƙaramin mu.


       —09-Juanury-2023

©...Ibrahim Y. Ibrahim ✍️

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post