Na Lura Mafiya Yawan Makiya Shek Abduljabbar Sun Fi Girmama Azzalumai A kan Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa'alihi.......!!!

 




@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@



... Umar Hassan Gololo... 

Kune a makale, a manne, a nanike da azzaluman shugabannin da suka jefa al'umma cikin bala'i da masifa. 

Duk zalunci, duk wauta, duk wauta, duk fasikanci, duk ta'addanci da dabbancin shugabannin Nigeria ba komai bane ba abin fada bane a wurinku, sai dai a kashe wane, a kashe wane da wane da ruwan kaulasan da shimmeruwa akan Musulmai shine abin da kuka fi zakewa kuna Zagin juna.  

Mun ji mun kuma karanta Maganganunku na wauta da rashin hankali da rashin tunani da hangen nesa akan addini domin ku biya bukatar miyagun shugabannin Nigeria. 

Wallahi Summa Tallahi wadannan miyagun Malaman sun fi ganin girma da darajar Gwamna da Iyalansa fiye da yadda suke ganin girma da darajar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Alihi da Ahlul-Baiti Alaihimussalam. 

Wadanne irin kalmomin kunyata musulunci da Musulmai ne baku furta akan wannan kazamar siyasar ba? 

Menene baku fada na rashin daraja da zubar da kimarku akan siyasar Buhari ba? 

Wace irin karya da abin kunya ne baku fada akan azzaluman shugabannin Nigeria domin ku gyara miyarku ba? 

Wallahi ko Shugaban kasa da Gwamna arna ne baku isa ku ce iyayensu suna wuta ko suna fitsari a tsaye ba, amma kuna jinginawa mafificin Halitta. 

Taronku, majarku da hadin kanku ba kuna yi domin ganin Shugabannin Nigeria sun samar da kayan more rayuwar al'ummar Nigeria bane, sai dai domin ganin bayan wanda ba kwa so. 

Tun lokacin da malalaciya kuma asararriyar Gwamnatin Buhari ta afkawa Malam Zakzaky(H) ta kashe Almajiransa da 'Ya'yansa muka fahimci lallai Malaman fada karnukan azzalumai ne. 

Muna rokon Allahu Ta'ala Ya ba wa Sheikh Abduljabbar mafita, Ya kubutar da shi daga Sharrin karnukan azzalumai, Ya kuma kunyata dukkan mai hannu da baki a cutar da shi Alfarmar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wa Alihi wa sallam.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post