Ko KasanDalilin Fitowar Nankarwa a Fata Musamman A Jikin Yar Macce..?


 

@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE. 


_By Dr Nazer Umar Muhammad...✍️ 

Daman ba iya mai juna biyu nankarwa ke fitowa ba?

Duba Abubuwa 10 Da Suka Kamata Ka Sani Game Da Nankarwa.

1. Nankarwa alama ce ta talewar fata. An fi ganinta galibi a tsatstsaye a kan fata. Kalar nankarwa ya dogara ga kalar fatar mutum.

2. Akwai shimfiɗu uku da suka haɗu suka samar da fata. A likitance, nankarwa na faruwa sakamakon talewar shimfiɗar fata ta biyu.

3. Galibi ta fi fitowa a kan fatar ciki. Sai dai wasu lokutan tana bayyana a kan fatar cinyoyi, nonuwa, ƙugu, damatsa da sauransu.

5. Nankarwa aba ce ruwan dare. Kuma tana iya fito wa kowa, maza da mata, babba da yaro, ba sai mata masu juna biyu kawai ba.

6. Waɗanda suke da sabuban fitowar nankarwa sun haɗa da:

i. juna biyu: Kaso 8 cikin 10 na masu juna biyu nankarwa na fito musu.

ii. waɗanda suke cikin shekarun balaga.

iii. Wanda ya rame ko ya yi ƙiba nan da nan.

7. Ga masu juna biyu, nankarwa na bajewa ko ta tsutstsuke bayan haihuwa.

8. Wasu nau'in mayukan shafawa suna iƙirarin magance nankarwa, sai dai babu ƙwararan dalilai da suka tabbatar da iƙirarin nasu.

9. A likitance, nankarwa, musamman ga masu juna biyu, ba ta da wata matsala. Sai dai idan akwai ƙaiƙayi ko kuma damuwa game da munin da nankarwar ke haifarwa ga fata, za a iya tuntuɓar likitan fata.

10. Har wa yau, a tuntuɓi likita idan nankarwa ta yi faɗi sosai tare da bayyanar tarun kitse / teɓa a ciki, wuya da ƙirji domin hakan na iya zama alamun wata cutar daban.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARAN MU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group din mu na Telegram Anan

👉 @MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/maasumahNews/

DOMIN BA DA SHAWARA KO AIKO DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post