Kaddarar Ka Rubutacciya Ce Tana Kuma Sauyawa !!![ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Bayan daukar dogon hutu tare da jingine wannan rubutun ,  yanzu wani dalili ya sanya tilas mu sake karkade shi, Mu ci gaba da karatu, 


Daga cikin Abin daukar hankali a cikin wannan rubutun shine haduwa ta da wasu mutane, 


 a cikin shafi na biyu da ya gabata, nace na dena yiwa mutane bincike saboda yadda muke qarewa a qarshe, mutane suna bin Ka ne kawai saboda buqatar kan su, daga ranar da Ka biya musu ita, daga ranar baka sake haduwa da su sai kuma wata matsalar in ta sake taso wa,, 


Bayan fidda wancan rubutun Wasu ba'arin mutane suka biyo ni inbox tare da magiyar cewa in yi haquri in duba qsunata ga ahlil kisa'i tare da duba girman Allah, na duba musu tafin hannun su, wannan tasa na yarda da roqon su sannan muka fara! A qalla na yiwa mutane sun fi talatin banda wadan da na a jiye a layi wasu na fara na bari wasu kuma banzo kan su ba,  Ina roqon duk wanda nayi wa kuma bai gamsu da yadda muka qare ba, ya fito ya qarya ta ni, wannan dama ce na ba shi, 


Bana kar6ar komai a hannun mutane sannan wasu sukan nemi zasu ba da kudi Amma nakan Dakatar da su,  


Wasu kuma in sun ji, Abinda ya basu mamaki sai suje su debo mini yan uwan su ko abokai suce suma suna roqon a temaka ayi musu,  har da wanda ya dauko mini mahaifiyar sa yana so ita ma abata bayanin tafin hannun na ta, 


sannan ko magani Ka nema a waje na in na San shi, zan iya hada Maka da kudi na da kuma lokaci na bazan kar6i ko kwabon ka, wasu kuma nine ma nake biyan kudin motar zuwa Garin da mutum yake yaje pack ya kar6a suma wadan da na yi wa haka suna da damar fitowa su qarya ta ni wannan ina yi ne domin gyara alaqa da mutum, to yanzu lokaci Yayi da nima zan fara kar6ar kudi a wajen duk wanda yake da buqata a waje na!  Yadda ko da Ka dena mu'amala da ni to dama Ka bayani haqqi na na koyi wannan ne a wajen wani inyamuri da Yayi wa blood brother din sa aski, shi kuma ya biya dhi! 


Na hadu da wata Hajiya da take fice fice zuwa wajen qasar nan kuma a fadin ta ta Dan San masu irin wannan ilmin ta ce ta samu abin mamaki lokacin da ta nemi mu hadu da ita mu tattauna, 


 na yi imani zata ga wannan rubutun Kamar yadda sauran da suka turo da hoton hannun su muka yi musu bayani,  suma zasu gani,  bayan tattaunawa masu me tsayi na yi Mata bincike ita kuma tayi referring dina zuwa ga wani film din Hindu Akan irin wannan binciken na tafin hannu,  GA poster din film din nan a qasa na saka ita ta turo mini da su,


 Lallai film ne na labarin soyaiya me kyau, sai dai rabin Abinda yake karantar wa a cikin film din qarin gishiri ne kawai domin labarin Yayi dadi, Baza kasan hakan ba, sai Ka San yadda ilmin yaje,

Ta yi mamaki matuqar gaske in ji ta yanda na Fitar Mata da cewa wacece ita?  Da fari ta dau abin wasa Amma daga qarshe ta daga hannu sama tace ta tuba! (surrender) saboda binciken ya fara zurfi yana barazanar ta6a Mata shaksiyya, sannan take fada mini cewa a kwai wannan ilmin yanzu Akan Internet kuma a yanzu haka ta soma yin karatun sa ita ma ,  

Lallai yin karatun a Internet zai temaka Maka wajen sanin wasu abubuwa, Amma zai kasance ne kamar in da zaka nemi Ka koyi yadda ake hada wayar hannu cellphone,  zaka samu komai Akan Internet,  Amma Shin zaka iya hadawar? Amsa gare Ka,

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post