Jagoran juyin Musulunci Na Iran Yayi Allah Wadai Da Wulakanta Al'kur’ani !!!

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Jagoran juyinmusulunci na kasar Iran Ayatullah Imam Khamana’I yayi Allah wadai da keta hurumin Al’kur’ani mai tsarki da aka yi a kasar Sweden da sunan hakki fadin albarkacin baki. Kuma ya zargi kasashe ma’abota girman kai da kokarin kai wa musulunci da al’kur’ani hari.


Har ila yau ya kara da cewa Al’kur’ani yana kara haskakawa ne a kullum kuma makomai mai kyau tana ga musulunci duk da makirce-makircen da kasahe ma’abota girman kai suke kullawa, ya kara da cewa ya zama wajibi dukkan masu neman yanci na duniya su goyon bayan musulmi wajen tunkarar mummunan makircin na yada kalaman batanci da nuna kyama ga ababen girmamawa na Addini


A gefe guda kuma kasashe da dama ne na duniya musamman a gabas ta tsakiya suka yi tir da wannan mataki na cin zarafin Alkur’ani da aka yi a kasar Sweden, inda wani mai tsattsauran ra’ayin adawa da musulunci yayi mai suna Rasmus Paludan a gaban ofishin jakadancin turkiya dake kasar,


Kasar Jodan Kuwait masa hadaddiyar daular larabawa Pakistan da sauran na daga cikin kasashen musumi da suka bacin ransu a fili game da wannan cin zarafin na littafi mai tsarki saukakke daga sama da musulmi ke girmamawa


𝙃𝙖𝙢𝙞𝙙𝙞𝙮𝙮𝙪𝙣 𝙋𝙧𝙚𝙨𝙨

26/𝙅𝙖𝙣/2023

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post