Hakkin Iyaye Bayan Rasuwar su Tamkar Hakkin Sune A Lokaci Da Suke Raye......!!!

 


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


     -Sheikh Adamu Tsoho Jos


Kayi Addu'a a mamaci kamar kana yuwa kanka yazo cewa bama kama bane kana yiwa kanka ne, mamaci ya zamo kamar sila ne na kai ka samu wani gafara da rahma sakamakon abinda zaka yi masa na addu'a don haka ko wani Abu na sadaka. Don haka abinda zanyi magana a yanzu duk wanda iyayen sa suka rasu to ya sani cewa akwai hakki mai girma a kansa. Musamman ita Uwa Da Uba wanda suka sha wahala akan mutum to kada ya zamo wani abu mai rudarwa ya rudar da mutum.


Ya kamata ace kullum kayi Sallah kada ka tashi sai ka musu addu'a, in zai yuwu ma in zaka iya duk wani motsi ka tuna dasu ka musu addu'a to ba zaka sauke hakkin su ba. To, amma in kayi kokari duk wani sallah da zakayi ko Sallah 5 din nan akalla Kulhuwallahu 3 din nan kace Allah ya kai lada zuwa ga kabarin mahaifiyata ko mahaifina a Kullum azahar la'asar magriba isha Asuba ya zamo cewa muna yiwa iyayen mu addu'a.


Shehin Malamin ya kara da cewa; Mun sha bayanin Mutum zai iya zamowa mutum kirki da iyayen sa amma bayan sun mutu, sai a rubuta shi cikin masu sabawa iyaye saboda mai ? Saboda ya manta da su. To, muna fatan ya zamo kada mu zamo daga cikin masu mantawa da iyayen su, kada mu zamo masu mantawa da 'yan'uwansu.


Kuma ya zamo ana Sadaka, kayi Sadaka kace ladan Allah ya kai ga Iyayenka, akwai Sallah da ake yi ga iyaye zakayi sallah da rana raka'a 2 Fatiha, Inna Anzannahu, a raka'an farko kenan. Sai Fatiha da Inna A'adaina Kalkausar, bayan kace Assalu Alaikum sai kayi Salati ga Annabi kace Allah ya kai ladan zuwa kabarin Mahaifiyata ko mahaifina.


In kuma 'Dan ka ko yarka ta rasu, ko 'ya'yan ka wannan karatun raka'oin su kaza karanta a sallah da zaka musu raka'a 2 amma shi ba'a yinsa sai da dare na yara kenan. Kuma jifa-jifa ana yin sadaka da iyaye.


 @ Sheikh Adamu Tsoho Ahmad Jos.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post