Gwarzon Shekara A Musabukar Alqur'ani Ta Kasa Ya Samu Karramawa A Jiharsa Ta Sokoto !!!

 



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]



DAGA Real Buroshi Mawaka Sokoto 


Wani matashi ɗan asalin jihar sokoto maisuna Nura Abdullahi Bello daga karamar hukumar Wamakko shine ya lashe gasar musabuka hizo 60 ta kasa wanda a tarihi shine karo na farko a jihar sokoto da ya samu wannan nasara a wannan matakin.


A yau ne akayi bukin Karrama shi wanda ya samu halartar manyan mutane da dama hadi da Gwamnan jihar sokoto Aminu Wazirin Tambuwal da mai alfarma Sarkin Musulmi Alh. Muhammad Sa'ad Abubakar 111 mni.


Kafin kammala bukin mai alfarma Sarkin Musulmi ya bada damar naɗa gwarzon shekarar da sarautar Modibbon Sokoto, sannan Mai girma gwamnan sokoto ya kara gwangwaje shi da Kujerar hajji guda hudu da naira milliyan goma da kuma ɗaukar nauyin karatun shi har zuwa matakin PhD a duk jami'ar da yake bukata.


Haka ma Nura Abdullahi zai sake Wakiltar najeriya a musabakar duniya da zata gudana a Saudi Arabia.


Muna Rokon Allah Yakara Bashi Nasara.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post