Faidojin Tsamiya da Amfanin ta a Jiki



Tsamiya na daya daga cikin ‘ya’yan itatuwan da al’ummar Hausawa ke amfani da su sosai a rayuwar su ta yau da kullum. Ta na da amfani mai tarin yawa, haka kuma ta na wasu illoli idan aka sha ta ba bisa ka’ida ba.

Ana amfani da tsamiya wajen sarrafa abubuwan sha, wajen yin magani, da kuma a girke girke a matsayin abun dandano.
Wannan cibiya ta bincike ta gano matsalolin da Tsamiya ke magancewa kamar haka:

1. Cushewar ciki da rashin yin bahaya

2. Mura da zazzabi

3. Ciwon ciki

4. Tashin zuciya ga masu ciki

5. Tsutsar ciki

6. Matsolin da suka shafi hanta da madaciya

 

ILLOLIN TSAMIYA GA LAFIYAR DAN ADAM

1. Tsamiya za ta iya haifar da illa ga masu ciwon sukari saboda ta na rage adadin sikarin da ke cikin jini. Haka ma ga wadanda za a yi wa tiyata, ana so su dakatar da shan tsamiya akalla makonni biyu kafin a yi tiyatar saboda wannan dalili.

2. Ga ramammu, yawan shan tsamiya na iya kara rama. Ga masu kiba kuwa za ta taimaka masu wajen rage kiba

3. Ba a son a sha tsamiya da magungunan Ibrofen da Aspirin saboda ta na kara adadin su da ke shiga jini. Idan haka ya faru, magungunan ka iya yin yawa su haifar da matsala.

 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post