Daukar Kan Imam Hussain (A's) Zuwa Birnin Alkahira(Misra).....!


[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Ya zo a Tarihin Faɗimiyyawa cewa : A rana mai kamar yau 8 ga watan Jumadha Thani shekarar 558H - Ranar Lahadi - Aka ɗauki Kan Imam Hussain (a.s) mai Tsarki zuwa Birnin Al-ƙahira daga Garin Asƙalan (Plastine) , tun bayan da aka ɗauke shi daga Karbala zuwa Kufa daga Kufa zuwa Sham har Plastine.


An Rawaito yayin da aka ɗakko Kan an sameshi bai gushe ba yana jiƙe da jini - duk da tazarar kusan Ƙarni biyar a tsakani -  kuma yana ƙamshi wane Almiski . 

Mutane sun ɗauki Kan ba takalma a ƙafafunsu daga Garin Gazza har Misra dan Girmamawa , har suka iso dashi Fadar Sarkin Misra a ranar Talata 10/Jumadha Thani/558H .

Hakan ya faru biyo bayan ƙoƙarin Sarkin nan da akewa Laƙabi da (Almalikus Shalih) na kashe maƙudan Kudaɗe dan ganin a dawo da kan Misra .


An rawaito karamomi dayawa sun bayyana daga wannan Kai mai Albarka , kamar yanda aka Rawaito har bayan an yanke kan Imam Hussain (a.s) kansa ya dinga Karanta Ayoyin Alkur'ani girmamawa daga Allah Ta'ala.


Amma a wajen Malam Shi'a Imamiyya (Ayyadallahu Burhanahum ) an dawo da kan Imam Hussain (a.s.)  Iraqi bayan an ɗauke shi daga Karbala zuwa gari-gari , an dawo dashi (Najaf ko Karbala) an sake binneshi kamar yadda yazo a ruwayoyi da zantukan Bijiman Magabatan Malaman Imamiyya Ithna Ashariyya .


السلام عليك يا أبا عبد الله الحسين 


✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post