Darajojin Sayyada Fatimatuz -zahara(s'a)A Littafan Ahlussunnah....!!!

 



                  




[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ] 


_Imam Zahbiy ya ruwaito ingantaccen Hadisi daga Manzon Allah (S) yana cewa; "Mafi soyuwar mutane a gareni ita ce Fatima!" Zahbiy yace ita Fatima ita ce yar auta a 'ya'yan Manzon Allah (S) mata, kuma ita ya fi so a cikinsu!" (Tarikhul Islam, na Zahbiy, 01-43).


       Imam Dabrany ya ruwaito Hadisi daga Manzon allah (S) yana cewa; "idan nayi sha'awar jin kamshin Aljanna sai in shaki kamshin  Fatimah (domin ita Hurul'in ce), ya Humairah! ita Fatimah ba kamar sauran mata take ba!" (Mu'ujamul Kabeer, na Dabrany, 02-401).


         Imam Hakim ya ruwaito Hadisi daga Ummul Muminina A'isha ta ce; "Ban ga wani mutum Wanda maganarsa ta fi kama da ta Manzon allah (S) kamar Fatimah ba! Ta kasance idan ta shigo wajensa yakan mikewa (dan girmamawa gareta), ya sumbaceta, ya yi mata maraba ya rike hannunta, ya zaunar da ita a mazauninsa!" (Al-Mustadrak, na Hakim, 03-160, Mu'ujamul Ausad, na Dabrany, Hadisi na 1014).

   Ummul Muminin A'ishah ta ce “ Ni dai banga Mutumin da yakai Fatima falala (da daraja) ba in ba Babanta ba!” (Mu'ujamul Ausad, na Dabrany, 03-349, Hadisi mai lamba 2742, Majma'uz-Zawa'id, 09-201).


Hakim ya ruwaito Hadisi cikin mustadrak dinsa, daga Manzon allah (S) ya ce; “Idan Alkiyama ta tsaya, mai kira zai yi kira ta bayan hijabi cewa;“ Ya ku taron mutane! Ku rufe idanuwanku daga Fatimah 'yar Muhammadu har sai ta (tsallaka Siradi) ta wuce!” (Mustadrak, na Hakim, 03-153).


    Imam Bukhari a Sahihinsa ya ruwaito Hadisi daga Manzon Allah (S) ya ce; “Fatima tsokata ce daga gareni, duk Wanda vya fusatata ya fusata ni!” (Sahihul Bukhari, Juz'i na 2, Kitabu Fadha'ilus-Sahaba, Babin Manakibul Fatimah (SA), Hadisi mai lamba 3767). )

  Abu Ya'ala da wasunsa sun ruwaito Hadisi daga Manzon Allah (S) yana cewa; “Ya Fatimah! Ki sani Allah yana fushi da fushinki, yana yarda da yardarki!” (Majma'uz-Zawa'id, 09-203, Mustadrak, 03-154).


Hakim ya ruwaito Hadisi daga Manzon Allah (S) yana cewa; “Fatima ce shugabar matan Aljanna!” (Mustadrak, 03-154, Musnad Ahmad, 01-293).


   Wannan kadan ne muka tsakuro daga dimbin hadisan falala da darajojin sayyida Fatimah (SA) a ruwayoyin da littattafan Ahlis-sunnah, kowace daya daga cikin ruwayoyin nan da muka kawo a matsayin misali, ta isa ta gamsar da mu girman daraja da buwayar sha'anin 'yar Manzon Allah (S) sayyida Fatimah (SA).


zamu ci gaba Insha Allah


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post