DAGA GARIN KATSINA; An Shiga Taron Mu'utamar Na Kasa A Garin Katsina

A yammacin yau Juma'a 27-01-2023 aka shiga taron  mu'utamar na kasa a garin Katsina, taron wanda dandalin Sisters da Academic Fora karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na kasa suka shirya. 


Baki daga sassa daban daban na cikin kasa Najeriya da cikin da damane suka halarci taron wanda ya fara gudana a yammacin yau Juma'a, an fara da rajista daga mahalarta taron daga bisani kuma aka shiga cikin taro.


An fara da bude taro da addu'a daga Sheikh Sidi Munir Sokkoto, sai karatun Alqu'ani daga bakin dan uwa Mujtaba Bilyaminu, sai kuma jawabin Maraba daga Malama Suwaiba Bauchi.


Yanzu haka jawabi na Biyu ake sauraro kan Maudu'i Bara'a da Wila'a daga Sheikh Rabi'u Abdullahi Funtua, dakin taro ya cika makil da mahalarta taron mu'utamar. Ga wasu daga cikin hotunan taron a Rana ta farko, ku ci gaba da kasancewa damu.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post