DA DUMIDUMINSA: Ba Mu Amince Da Karin Wa'adin Daina Karbar Tsoffin Kudade Ba, Dole Sai Shugaban Babban Bankin Nijeriya Ya Bayyana A Gabanmu, Cewar Majalisar Tarayya




...dole sai an kara wa'adin zuwa 1 ga Yuli, 2023, cewar majalisa


Shugaban masu rinjaye a majalissar tarayya Rt, Hon Alhassan Ado Doguwa wanda majalisa ta naɗa akan shine wanda zai zauna da gwamnan babban banki Emifele tare da manyan manajojin bankuna domin gano yadda matsala take ya ce ba su amince da ƙarin da gwamnan babban banki ya yi ba na ƙara kwana goma. Sun ce ya zama dole ya bayyana a gaban majalissa ranar Talata domin amsa tambayoyi akan wannan canji da gwamnati za ta yi.


Hakan na zuwa ne bayan da Gwamnan babban banki ya gana da Shugaban ƙasa a yau Lahadi a garin Daura dake jihar Katsina.


Sannan majalisa ta sha alwashin dole a ɗaga wannan al'amarin canjin har zuwa 1 ga watan Yuli domin kada tattalin arziƙin ƙasar ya cigaba da komawa baya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post