An samu ɓallewar wata cuta a garin Kano mai suna “Diphtheria” !!!

 [ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Assalamualaikum warahamatullahi taala wabar katu hum barkan ku dai maza da yammata masu bibiyan mu akan wannan website me suna herwagana.com,


Yana da kyau a gaggauta ɗaukar duk wani mutum da yayi ƙorafin yana fama da bushewar maƙogaro, tari, ɗaukewar yawu, sauyawar murya, kumburin wuya, numfashi ba daidai ba, zazzaɓi ko warin baki zuwa asibiti.”


Cutar tana tokare kafar shige da ficen iska kuma tana hana mai ɗauke da ita yin numfashi, har ma a ƙarshe ta kashe shi.


Yin magani cikin gaggawa yana da matuƙar amfani domin kiyaye mai ɗauke da wannan cuta daga mutuwa ko naƙasa.


Cuta ce da take bin iska, don haka tana yaɗuwa ta hanyar tari, atishawa ko haɗa jiki da mai ɗauke da ita.


Domin kiyaye kai, ayi rigakafi ga wanda ba’a yiwa ba, da amfani da “toxin booster” ga wanda aka rigaya aka yiwa rigakafin, sannan a taƙaice haɗa jiki da masu ɗauke da cutar.


Allâh ta’âlâ ya tsare mu baki ɗaya, ya bawa masu ɗauke da cutar lafiya. Amîn.


Rubutawa: Dr. A.I Sabo.


Muna godiya da kawowar ku ziyara cikin website din mu me suna herwagana.con wadda muke nemo muku sahihan labarai masu inganci karku manta da ku danna mana kararrawa a gefen hannun ku ta dama ta kasa zaku ga kararrawar.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post