An Gina Wani Katafaren Kamfanin Shinkafa Da Shine Mafi Girma A Dukka Nahiyar Africa Mai Suna Mangal Rice A Jihar Katsina.




Attajirin Ɗan-kasuwa shugaban kamfanin sufurin jiragen sama na Max-Air da kamfanin gine gine da tsare tsare na Afdin Construction Alhaji Ɗahiru Barau Mangal, ya kammala aikin gina katafaren kamfanin shinkafar da yake ginawa a jihar Katsina mai suna “Mangal Rice” wanda za a riƙa fitar da shinkafa tan dubu 300 a kowace rana. 


Kamfanin ya tsaftace shinkafarsa ta yadda za tayi gogayya da kowace irin shinkafa a duniya. inda a yanzu za a fara fitar da Shinkafar a kasuwannin duniya. 


Haka zalika a cikin kamfanin an samar da bangaren yin takin zamani mai ƙyau "Gobarau Agro Fertilizer” domin amfanin manoman rani dana damina.


“A cewar Babban daraktan kamfanin Alhaji Fahad Dahiru Mangal , ya ce kamfanin zai riƙa fitar da shinkafa tan dubu ɗari uku 300,000 a kowace rana. 


Kamfanin ya laƙume kuɗi har kimanin biliyan 20b. inda zai samar da ɗinbin guraben ayyukan yi ga matasa har mutun dubu goma tare da bunƙasa tattalin arziƙin jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya. 


Allah Ya ƙara bamu zaman lafiya  a Najeriya baki ɗaya.

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post