Zagin Sahabbai Da Fada Da Sahabbai Ba Ridda Ba ne Ya Kama A Gahimta- Prof Ibraheem Makari..!




[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]

 sahabbai da fada da sahabbai ba ridda ba ne yakamata mu fahimci wannan da kyau, zai iya zama ridda idan ya zama wani abu ne wanda ya zama Ma'alumun minat deeni biddarura mutum yayi inkari kamar yanzu misali sai mutum yace Sayyadina Abubakar ba Sahabi ba ne me yasa wannan ya zama ridda?


Sabo da Allah ne ya kira sayyadi na Abubakar sahabi ina fatan mun fahimta, ko kuma mutum ya tuhumi Nana Aishe da abinda Allah ya barrantar da ita da shi kur'ani yace batayi ba kai kace tayi wa'iyazubillah.


Amma ba mujarradin zagin sahabi ba zagin sahabi khabira ce kunsan khabira ko? Daya daga cikin khaba'er manya manyan laifuka to amma su masu fada da Abdujjabar suna nema su dauke wannan abin a wannan matsayin sabo da wani dalilin su su kuma, dalillin shi ne.


Sabo da rigimar dake tsakanin Ahalussunnah da Shi'ah to sai ake kokari ayi amfani da wannan damar ayi talhikin abin, a maida shi cewa Manzon Allah Saw yake zaga to ni ina ganin wannan shi ma ba abinda yafi dacewa ba ne.


Malamin ya ƙara da cewa, babu wata hujja da ke nuna cewa idan mutum ya zagi Sahabbai ko yayi faɗa da su shikenan ya fita daga musulmin wato yayi ridda

- B B C Hausa


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post