Yan Shi'a ne Masoya Sahabbai Na Gaskiya!!![ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Wanda yace : Duk Sahabban Annabi ba mutanen kirki bane shine mutumin banza kuma ya halaka ya taɓe , kuma wannan ba ita bace Aƙida da Matsayar Shi'a game da Sahabban Annabi (saww) .

Wanda yace : Sahabban Annabi (saww) baki ɗayan su Adalai ne na gari ne ya saki layi , domin hakan ya saɓawa Waƙi'i da Nassin Alkur'ani da Hadisai da Sirar Sahabban , babu shakka wannan ma ba matsayar ƴan Shi'a bace game da Sahabban Manzon Allah (saww) , domin Sahabbai kashi-kashi ne kuma hawa hawa ne , akwai Uduulun akwai kuma akasin haka .

Babu wanda ya isa ya musa haka sai Jahili ko kuma mutum kangararre munkiri .

TO MENENE MATSAYAR ƳAN SHI'A GAME DA SAHABBAI ???

A ko da yaushe maƙiya Shi'a da Shi'awa sukan ƙoƙarin ɓata su da nuna su a matsayin wasu maƙiya Sahabbai ko wasu mutane da basa ƙaunar duk Sahabban Annabi (saww) , wanda wannan tsantsan rashin Adalci ne ga ƴan Shi'a, domin ba ita bace Aƙidar su game da Sahabbai , ƴan Shi'a basa yiwa Sahabbai kuɗin goro su zage su ko su kafirta su ko su aibatasu kamar yanda aka ruɗi dayawan jahilai da wawaye da hakan , wasu an musu gadar zare suka faɗa , wasu kuma suna yine da gangan da ganganci , suka ɗauki zagin Sahabbai a matsayin wani makami da zasu yaƙi Shi'a dashi a wajen jahilan mutane da basu san Shi'a ba .

Ƴan Shi'a suna ƙudurce cewa Sahabban Manzon Allah (saww) sun kasu kamar haka ;

1 . Daga Sahabbai akwai Adilai, Muminai , Waliyyai , Salhai da suka kai wani matsayi a wajen Allah da ba masanin haƙiƙanin sa sai Allah da Manzonsa . 
Tabbas Waɗannan sun rabauta duniya da lahira , kuma zama da Manzon Allah ya amfane su cikin taikonsa da yin imani na haƙiƙa da shi , Radiyallahu Anhum Wa Radhu Anhum .
Duk sanda kaji an yabi Sahabbai ko an jinjina musu a cikin Alkur'ani da Sunna to da wannan kashi ake .Ƴan Shi'a suna ƙaunar waɗannan Sahabbai, suna neman alabarkarsu dare da rana kuma Adilai ne ko shakka babu 

2. Akwai kuma akasin kashi na farko , Waɗanda zama da Annabi (saww) bai amfana musu komai ba , saboda rashin Imaninsu da shi Imani na haƙiƙa da taimakon sa da riƙe alƙawari a bayan sa , bari ma sun cutar da shi cutarwar da ba'a yiwa wani abun halitta kamarta ba a cikin halitta .
Duk inda kaji suka ko allawadai da sashin wasu Sahabbai a cikin Alkur'ani mai girma to dasu ake , irin su ne aka rawaito Annabi (saww) yace : A cikin Sahabbai na akwai munafukai goma sha biyu na za su shiga Aljanna ba , irin su ne suka dinga shirya kashe Manzon Allah (saww) lokaci bayan lokaci har a ƙarshen rayuwar sa , irinsu ne suka assasa cutar da iyalansa a bayansa har aka kai ga halin da ake ciki a yau , irin su ne irin su ..... Tarihi ya sajjala ayyukan su da halayen su .
Ahmadu ɗan Hambali ya rawaito a cikin Musnad , Manzon Allah (saww) ya ce : A cikin Sahabbai na akwai wanda bazai ƙara gani na ba har Abada . ma'ana dai daga ƙabarinsa sai wutar Jahannama.
A ruwayoyin Bukhari da Muslim kuwa , Akwai wadanda sai anzo dasu Annabi (saww) ya gansu a ranar Alkiyama sai kuma a korasu Wuta , har ya dinga ya Ubangiji Sahabbaina ne Sahabbaina ne , Sai ace ai sun sauya a bayanka.

3 . Akwai kuma Waɗanda Allah da Manzonsa ne kawai suka san halinsu a Duniya da lahira , suna cikin kashin farko ne ko na biyu ? Tarihi bai hakaito wani abu akansu a rarrabe ba ballantana ayi naƙadin rayuwarsu , koma sam ba'a san sunansu da halayensu ba . Domin gabaƙi ɗaya Sahabban da aka yi Tarjamarsu a littattafan Tarajimu basu ne Jumlar Sahabban Manzon Allah (saww) .
Shi yasa akwai abun mamaki tattare da masu yiwa Sahabbai Kuɗin goro da Adala da Imani na gaskiya , ta yanda suke yin hukunci akan abinda basu san shi ba basu san halinsa ba , wato dai suna yin hukunci akan Majhuli . Uwa uba ma yadda suke sabawa hankali , Ayoyin Alkur'ani, Hadisai , Waƙi'i da Sirar Sahabban Kansu a cikin hakan .

A taƙaice dai ƴan Shi'a suna rarrabe hukunci da matsayar su dangane da Sahabban Manzon Allah (saww) , matsayarsu matsayar Alkur'ani da Sunnah ce game da Sahabbai , basu gaza ba a cikin haƙƙin su kuma basu wuce gona da iri ba kamar yanda wasu suka yi , Basu yadda da ƙa'idar "Kullhum Uduulun ba" Kuma ba sa cewa "Kulluhum Kuffarun wa Fusuuƙun " suna bibiyar tarihi da abinda ya tabbata na rayuwar Sahabbai bisa ma'aunai na Shari'a, su ƙaunace su don Allah da gaskiya ko su ƙyamaci aikinsu don Allah da gaskiya . Batun gaskiya da gaskiya ƴan Shi'a basu da wata maslaha ta musamman cikin so ko ƙin Sahabbai .

Abun takaici shine yadda maƙiya ƴan Shi'a suka cakuɗa waɗannan mas'alolin da gangan don su ɓata ƴan Shi'a .
Ba komai yasa ba za su yarda da Aƙidar ƴan Shi'a game da Sahabbai ba sai dan hakan zai lazimta rushewar Aƙidar su da Addinin su baki ɗaya game , wanda wannan Aƙidar tasu itace ainihin ƙin Sahabbai da zaluntar su , ko Sahabban ba za su yarda da wannan Aƙidar ta "Kullhum Uduulun" bari ma sun ƙaryata ga duk wanda ya bibiyi tarihin rayuwar su , don haka ne ma muka ce ƴan Shi'a ne masoya Sahabbai na gaskiya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post