Yadda zaka dawo da WhatsApp dinka da akayi Banned ko hakin baki daya.

 Assalamu alaikum barka da tau barka da kasancewa da SIRRIN ANDROID.

A rubutun namu na yau zanyi bayanine akan korafin da mutane da yawa sukeman kwanan nan na cewa anyi banned numbernsu daga amfani da whatsapp, wasu anmasu hakin ne wasu kuma sakamakon manhajar whatsapp ta hana amfani da GB wasu kuma wani dalilin ne na daban.


To inshaallah idan kabi wannan process din kowannensu ne daga ciki a cikin awa24 zasu budema numbanka zakaci gaba da amfani da ita kamar yadda ka saba.

Da farko ana buqatar wayar da zakayi amfani da ita ya kasance akwai browser ko opera akai, zaka shiga cikin google ka danna alamar search ka rubuta

👇

Whatsapp Contact

Sai kayi search, sai ka za6i na fari wanda shine nayiwa arrow a wannan photon da ke qasa, shigarka keda wuya zakaga FORM inda zaka zabi kasar da kake, bayan ka za6a dai ka rubuta wannan numban da kamfanin whatsapp suka hana kayi amfani da ita, bayan ka shigar da numban sai ka rubuta email dinka a kasa, ka qara maimaita shi inda aka rubuta "Confirm Email Address" bayan ka rubuta zasu baka za6uka kamar haka

👇

Android

iPhone

Web and Desktop

KaiOs

Others

Sai ka za6i wayan da kake amfani da ita kafin su rufe numban, idan da computer kake amfani sai ka za6i (Web and Desktop) bayan ka za6a zakaga inda aka rubuta "Please enter your message below" ma'ana ka rubuta saqon da kakeso ka isar zuwa ga kamfanin whatsapp, sai ka rubutamasu cewa anyi hakin account dinka kanaso ka dawo da account dinka, idan banned din numban akayi shima zaka gayamasu cewa anyi banned numbanka daga whatsapp kuma baka amfani da GB whatsapp ko makamancin haka.

Sai kawai ka danna inda aka rubuta "NEXT STEP''

Bayan ya bude sai ka duba daga kasa zakaga "SEND QUESTION" sai ka danna gun, sai kawai ka jira 24 zuwa 78 hours zasu budema numbanka.


Ba iya wannan kadai ba, zaka iya amfani da wannan process din idan ka manta 2FA na whatsapp dinka

Allah yasa mu dace🙏

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Idan kayi kuma be dawo ba fa yazakai dan allah

    ReplyDelete
Previous Post Next Post