Wasu Abubuwan Burgewa Game da Mace...!
@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE 

Wasu Abubuwan Burgewa Game da Mace.                    

1: Mace tana cikin tsananin damuwa, amma da zaka tambayeta yaya take zata ce maka lafiya take batada matsala. 

Haka kuma idan Mace ta fito fili ta fadamaka Matsalata ba tana fadamaka bane domin ka taimaka mata ba sai domin ta aminta dakai ne tana neman kalmar da zai kwantar mata da hankali daga gareka.

Mata sunada zurfin ciki, hakan yasa muddin namiji bazai yi amfani da yakamata ba zai jima yana kuntatawa matarsa, kanwarsa, budurwar sa ko mahaifiyarsa bai sani ba.

Mata suna fadawa mutumin da suka yarda dashi kuma sukasan zai biya musu bukatunsu na matsalar su ne amma ba kowa ba.

2: Mata a kowani lokaci a kowani yanayi suna cikin bukata ne. Hakan yasa mata sun fi maza yawan tunani.

Mata sukan dauki matsalolin daba nasu ba su daurawa kansu. Haka nan suna son yin rayuwa fiye da samunsu. Wannan yasa a kullum cikin bukata suke a kullum cikin matsala da damuwa suke.

3: Duk wata mace tana daukan kanta kyankyawa ce. Amma kuma kashi 2 ne cikin 10 na mata suke fitowa gaban mutane suyi ikirarin suna da kyau.

Duk kyan mace idan kace mata tanada kyau sai taji dadi a ranta. Haka duk munin mace ta tsani ka ce mata mummuna, amma ita tana iya fadawa kanta da kanta ita mummunace amma da wani zai fadamata bazata so ba.

4: Mata sunfi yawan tunanin ko kuma son kusanci da mutanen da basu damu dasu ba.
Ga inda ake tarairayan mace, tafi so taje inda itace zata yi tarairayan.

5: Mace ta tsani ka kwatanta ta da wata macen. Ka nuna wacce ta fita da wani abun. Amma mace ita da kanta zata iya fadamaka wacce ta zarce mata a wani abun. Idan sune suka fada da kansu hakan bai musu zafi maimakon wani ya nuna cewa wata ta fita.

6: Mata sunfi maza dauriya idan suna ciwo. Hakan yasa sukafi maza yawan lalura.

Da Allah (SWT) Ya halicci mata da yawan laulayi, sai kuma ya musu baiwar jimirin ciwon.
Cutan da zai saka mace kuka idan na miji ya kamu dashi sai suma, da raki.

7: Mata sukan dauki lokacin kamin su yarda ko su gamsu da abu. Kamin su dau mataki akan wani lamari su rika jan lokaci, amma daga lokacin da suka fidda matsaya akan lamarin za a jima kuma ba iya sauyawa musu ra'ayi akan wannan matsayar tasu ba.

8: Mata suna son ganin namiji mara tsoro ko shakka. Mace da zaran ta hadu dana miji mai irin wadannan halayen nan, take yake shiga ranta koda ba soyayya zasu ba zata ji ya kwanta mata a rai.

9: Mata sunfi samun kwanciyar hankali da natsuwa idan suna mu'amala da maza fiye da 'yan uwansu mata.
Duk mace tana son taga akwai wani namiji na musamman da yake bata shawara a duk lokacinda bukatar hakan ya taso.
Sai dai abun mamaki anan mata sunfi daukan shawaran iyayensu mata akan iyayensu maza.

Mace zata iya fita waje ta nemi shawaran wani namijin amma bazata iya nema a wajen Uban da ya haifeta ba, amma fa qalilanne masuyin hakan.

10: Ba kamar maza ba, mata suna bukatar akalla mintuna 30 kamin bacci ya dauke su, ba kamar namiji da zai iya kwanciya nan take ya kama bacci ba. Su mata a lokacin da suka kwanta bacci a wannan lokacin suke tilawar abubuwan da suka faru a wannan ranar wannan tunanin shike sasu daukan lokaci kamin suyi bacci. 

 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post