Tamkar yadda mutum ke da dangantaka da Aljan a halitta, dabi'a da kuma yin addini, to haka ma musulmai ke da dangantaka da Kiristoci.




DANGANTAKAR MUSULMAI DA KIRISTOCI



Tamkar yadda mutum ke da dangantaka da Aljan a halitta, dabi'a da kuma yin addini, to haka ma musulmai ke da dangantaka da Kiristoci.


Don kankare tsatsar da ke cikin qwaqwalen masu cewa 'yan Shi'ah addininsu iri daya ne da kiristoci, bari mu leqa cikin littafi mai tsarki mu gani ko su ma za su fice faga cikin wannan dangantakar?


Allah mai girma da daukaka na cewa,

" LALLE ZA KA SAMU MAFIYA TSANANIN MUTANE A ADAWA GA WADANDA SUKA YI IMANI, YAHUDU NE DA WADANDA SUKA YI SHIRKA.  KUMA ZA KA SAMI MAFIYA KUSANTARSU A SOYAYYA GA WADANDA SUKA YI IMANI SUNE WADANDA SUKA CE , " LALLE MU NE NASARA (Kiristoci) ." DOMIN KUWA DAGA CIKINSU AKWAI QISSISINA DA     RUHUBANA (Malamai da masu bautar Allah a kebe). KUMA LALLE NE SU BA YIN GIRMAN KAI (wajen karbar gaskiya) ."


" KUMA IDAN SUKA JI ABINDA AKA SAUKAR ZUWA GA MANZO, KANA GANIN IDANUWANSU NA ZUBAR DA HAWAYE SABODA ABINDA SUKA SANI DAGA GASKIYA, SUNA CEWA, " YA UBANGIJINMU ! MUNYI IMANI, KA KA RUBUTA MU TARE DA MASU SHAIDA ."


(Ma'ida:82-83)


Manzon Allah (S.A.W.W) na cewa, " BAYAHUDE BA ZAI TABA HADUWA DA MUSULMI BA FACE ZUCIYARSA TA RIYA MASA CEWA YA KASHE SHI ."


======== NAZARI =======

______________________________________


A lokacin da Kafiran Makkah suka tsanantawa Annabi da Sahabbansa sai ya tura su Hijra zuwa Habasha qarqashin jagorancin Ja'afar Bn Abu 'Dalib (A.S) zuwa ga Sarki Najjashi.

To, da ya ji bayani daga gare su sai ya fashe da kuka saboda qaunarsu.


Hakama a yanzu da Gwammatin Zalunci ke karkashe 'yan Shi'ah, to Kiristoci su suka fi fitowa suna nuna rashin goyon bayansu da rashin amincewarsu, yayin da wasu gurbatattun Musulmi 'yan'uwan Yahudu ke goyon baya.


Ni dai ban ga hanyar rarrabe wannan dangantakar ba, sai dai ga wanda ya kasance Kafiri ga ayoyin Allah.

Daga wakilanmu na Zone din Bauchi, Gombe da Adamawa.


Tare da (Ado Isah Guda)


08137925034/08126385470

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post