Ta'addancin Kisan kiyashin Zaria A 2015



 @MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE


Da fari ya kamata ne mu tambayi kawukanmu, wai yaushe ne aka fara zubda jini a Arewa?! An fara zubar da jini ne a Arewa tun shekaru aru-aru da suka gabata, amma mummunan zubar da jini na nan kusa-kusa shi ne zubar da jinin ƴan Shi'a wanda Manjo-Janar Buhari yayi a Zariya (2015). 

Wannan shi ne mummunan ta'addancin da yankin Arewa bai taɓa ganin irinsa ba, ta'addancin da ko a yaƙin Basasa ba a yi shi ba. To, tun a wannan lokacin ya kamata duk mutane su fito su ƙalubalanci zaluncin Buhari na zubar da jinin ƴan Shi'a. Amma abin takaici sai mutane suka yabi hakan, sukai murna suka ji daɗi da hakan, sukai shewa suka tafawa waɗanda sukai wannan ta'addanci. Wannan kuma shi ne dalilin da ya kawo mu ga halin da muke ciki yau a Arewa.

Domin in baicin irin murna da jin daɗin #KisanKiyashinZariya da ƴan Arewa suka yi, babu yadda za ai Buhari ko wani ɗan ta'adda ya samu damar ci gaba da zubar da jini a Arewa. Hakan ya ƙara wa Manjo damar ci gaba da kallon ɗan Arewa a matsayin wawan mutum wanda bai san abin da yake yi ba. Wannan ne ya baiwa ƴan ta'adda damar ci gaba da kashe mutane a Arewa kamar awaki. Domin su ƴan Arewar ne suka nuna cewa dabbobi ma sun fi wasunmu hankali, tunani mai kyau da sanin darajar ran ɗan'adam, a yi haƙuri bawai ina nufin mu dabbobi ba ne. Amma abin da wasunmu sukai ko dabba bai dace tayi hakan ba. 

Daga lokacin kuwa da aka wa ƴan Shi'a mummunan kisan kiyashin kuma ƴan Arewa sukai murna suka buɗe hanya da kafar ci gaba da zubar da jinin ƴan Arewa kuma a Arewar, daga wannan lokacin ya zama tamkar sun bada 'tickets' ɗin shigowa a ci gaba da zubar da jini a Arewar. 

Ko kana ganin ƴan Shi'a sun aikata laifin da ya dace ai masu #KisanKiyashi ne? Bari na baka misali. Ita wannan lalatattar gwamnatin wacce bata san inda ta dosa ba, a ƙasar nan muna ji muna gani ƴan ta'adda suna kashe mutane, suna ɓarnata dukiyar al'umma da dukiyar gwamnatin ƙasar, su kashe mutane, su kashe jami'an tsaro, amma har yau gwamnati lallashinsu take, ana nemansu ana sulhu da su ana kuma basu maƙudan kuɗaɗe, don me za a dinga bin ƴan Shi'a ana kashe su alhalin basu yi ko ɗaya daga cikin waɗancan abubuwan da waɗancan ƴan ta'addan ke yi ba? 

Irin yadda gwamnatin ke neman sulhu da ƴan ta'adda mai zai sanya baza ta nemi sulhun da ƴan Shi'a ba domin a kaucewa ci gaba da zubar da jini ba? wani laifi ƴan Shi'a suka aikata da har za a ce baza ayi sulhu da su ba? Idan gwamnati na sulhu da ƴan Boko-Haram, Kidnappers da Arms bandits mai zai hana tayi da ƴan Shi'a, ko kuwa tana nufin ƴan Shi'a sun fi ƴan Boko-Haram laifin ne? Ko kuwa sun fi Kidnappers da Arms bandits laifi ne? 

Idan kafa gwamnati cikin gwamnati ne akwai wanda yakai ƴan ta'addan nan kafa gwamnati? Wanda su bama gwamnati ba kashe mutane da jami'an gwamnatin suke, su tare hanya su kashe mutane, su ƙwace dukiyarsu, su yi garkuwa da wasu da neman kuɗin fansa, sannan su kai hari su karkashe mutane su ɓarnata dukiya, su yiwa mata fyaɗe su sace wasu. Amma duk da haka kullum gwamnati ta na lallamarsu da roƙon su zo ai sulhu, mai zasa ba zata nemi Islamic movement da irin wannan sulhun ba? 

Wannan zai nuna mana cewa ita gwamnatin nan bawai muradin talakawa ba ne a gabanta, ba ci gaban ƙasar nan take nema ba, burinta kawa shi ne ta jefa talakawa a cikin wahala da masifa. Matuƙar kuwa mutane basu tashi sun jajirce kan matsalar tsaron nan ba, haka za a ƙarar damu da da irin wannan kisan da ake mana na ɗaya bayan ɗaya. 

Su kuma sauran (majority) na ƴan Arewa masu murna idan an kashe ƴan Shi'a ba zan ce su dena ba (jiki magayi), su ci gaba da murna, idan yau an kashe wasu kayi murna ka kwana da sanin cewa gobe kai ne za a kashe da iyalanka, kuma in an kashe ku an kashe banza an kashe wofi, babu wanda zai kula, kuma babu wanda zai damu da kashekun da akai Allah yasa al'ummar Arewa mu hankalta.
 
#JusticeForZakzakyNow. 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post