Shayin Rage Kiba Na (4)...!!!


 @MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE  

INGREDIENTS:


1. Kanunfari (clove)

2. Citta (ginger)

3. Habbahan (cardamom)

4. Girfa (cinnamon)

5. Cumin

6. Na'a Na'a (mint)

7. Zuma (honey)

8. Masoro (black pepper)

9. Ganyen shayi irin wanda kike da shi.

Ni zan saka Green tea, top tea, sai wani da na ke sha da yake reducing sugar a jiki.


PROCEDURE


: Bayan kin samo abubuwan da na lissafa, wanda wasu ana samun su a kasuwan gargajiya wasu kuma gaskiya sai a supermarket. Ba wai dole sai irin nawa ba, in dai sunan ďaya ne shikenan domin ko wane kamfani akwai nashi. Sannan wadanda ban sanya sunansu da hausa ba to ban sani bane na turancin kawai na sani. Green tea na kan yi amfani da na tea bag ko kuma wanda aka busar da ganyen aka yi packaging.


Haka nan citta ma na kan sa gari ko danye ko na haďa biyun, haka ma cinnamon da sauran. Kamar yanda zaki dafa shayi haka zaki yi masa. Ki zuba ruwa a tukunya sai ki zuba dukkanin abubuwan, amma kada ki cika su da yawa. Musamman in kina da ulcer zai kasa shawuwa miki, komai ki sanya shi ďan dai-dai.


Daga nan sai ki bashi lokaci ya dahu. Sai a tace bayan an sauke, sai a zuba zuma ko sugar. Ni dai duka biyun nake haďawa, sannan plz kada ki cika masa sugar sosai saboda shayi ne mai lafiya da dadi. In ana sha sugar bai ji ba sosai ya fi daďi. Idan zaki yi irin wannan shayin ki yi kokarin nemo cardamom garinsa ko kwayoyinsa domin yana da kamshi mai mutukar dadi a shayi. Kina zuba kwayoyi biyar ma ya isa.


Wuni zaku yi kuna sha, a yi a juye a flask ana sha. Ban da qara lafiya zai saukar miki da ni'ima da qara dadi hajiya, hatta infection in kina dashi zai iya kashe miki. Sai an gwada akan san na kwarai. Wannan shine haďi na farko wanda in dai kika masa sai ya san an dafa masa shayi wanda bai saba sha ba. Kuma daga ranar zai rinka siyowa da kansa don a masa. 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post