Shahadar Sayyida Fatima Az-Zahra(SA)!!!


 @MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE 


Yau 13 Ga Jimadal Ula, daya ne daga ranakun da ake jaje da Juyayin Shahadar Sayyida Zahra (SA).

Akwai ruwaya da ke nuna cewa Sayyida Zahra (SA) ta yi Shahada ne bayan Shahadar babanta da kwanaki 75 ko 95. Don haka sai ake raya duka raneku biyun, wanda na farko na kamawa 13 ga Jimadal Ula ne, na biyu kuma yana kamawa ranar 3 ga Jimadal Thani ne.

Sai dai a na kwanaki 75 din, a kan dauki kwanaki uku ne a yi jajen, wato ranar 13 da 14 da 15 ga Jimadal Ula, don ya zama ko da an samu naƙasar cikan wata ko watanni biyu daga Safar zuwa Jimadal Ula din, to akalla dai za a dace da kwanaki 75 din daidai wajen raya munasabar.

Shahadar Sayyida Zahra Amincin Allah A Gareta wani abu ne da ya kasance bayan zalunci mai girma da aka yi mata. Zalunci nau'i-nau'i, na farko yadda aka zalunci mahaifinta a lokacin jinyarsa aka rika masa hargowa da fada masa baƙar magana da gatse, da yadda daga karshe ma aka masa ɗure alhali yace baya so, wanda ana tunanin wannan ya taimaka ga Shahadarsa.

Na biyu kuma yadda bayan Wafatin mahaifin nata, aka kwace hakkin mijinta na Shugabancin Musulmi, bayan ManzonAllah (S) ya halifantar da shi a gaban dubban Sahabbansa a Ghadeer Khum, sannan kuma aka bi shi da cutarwa da dira masa a gidansa, wanda hakan ya yi sanadiyyar afka mata.

Na uku; kwace mata hakkinta da aka yi na Fadak, ta nema da sunan kyauta ce da mahaifinta ya bata, ta gabatar da shaidu amma duk aka hana ta. Ta nema da sunan in ba a yarda nata bane, to a bata a matsayin gadonta, a matsayinta na 'Yar tilo da Manzon Allah (S) ya rasu ya bari, amma shima Halifa yace wai ya ji Manzon Allah (S) yace, su taron Annabawa, ba sa gado kuma ba a gadonsu. Wanda da wannan ya fake ya hana ta hakkinta bisa zalunci. Tare da cewa yar Halifan ta yi Da'awar dakin da Manzon Allah (S) ya rasu na cikin gadonta, don haka ma ta yarda aka bizne Babanta da Amininsa a cikin dakin, ta ki yarda a bizne babban jikan Annabi (S), Imam Hasan (AS) a cikinsa.

Na hudu; yadda tarihi bai boye ba sam, cewa an dira ne a gidan Sayyida Zahra (SA), aka banka wuta a gidan, wani ya bugi ƙyauren dakin Sayyida Zahra (SA) da kafarsa, karfen da ake tokare kofar ya dawo ya caki kirjin Sayyida Zahra, ya karya ƙashin Awazanta, ya kuma ɓarar da cikin da take da shi na Sayyad Muhsin, sannan ya shiga da mutane dakin suka saka bulala suka rika dukanta, bayan sun tafi da mai gidanta don ya wa halifa bai'a, hakan ya ja mata jinyar da shi ya zama sanadiyyar Shahadarta.

Na biyar; yadda ya kasance, gudun kar a tone Kabarin Sayyida Zahra (SA), ta wa mijinta wasiyya, Imam Ali (AS) ya bizne ta da daddare, ya ki bari duk wadanda suka cutar da ita, ciki har da Halifofi su sallaci gawarta ko su shaidi bizne ta, sannan kuma ya boye Kabarinta, har yau ba a san inda yake ba a hakika, sai dai an ce mutane na kaddara Kabarin Sayyida Fatima Bint Asad, mahaifiyar Imam Ali (AS) a matsayin shine na Sayyida Zahra (SA) a Baƙi'a.

Ko da Manzon Allah (S) ya yi Shahada, ya tafi ne ya bar tsokar jikinsa a cikin al'ummarsa, amma a yayin da al'ummarsa ta kashe tsokar jikin nasa, sai ya zama ta rabu da shi baki daya a ganin zahiri, wadanda suka wanzu tare da shi a hakika sune wadanda suka kasance masu riko da Iyalan gidansa a bayansa, masu tausaya musu musibar da suka gani, masu nuna tawaye ga makasansu da wadanda suka cuta musu, masu kokarin dabbaka irin aikin da Shugaba (S) ya aikata a doron kasa na kafa shari'ar Allah a cikin al'umma.

Ina jaje ga dukkan Muminai na rashin Shugabarmu Sayyida Zahra (SA) a irin wannan lokacin. Allah Ya girmama ladanmu bisa wannan musiba da dacinsa ke mana radadi a zukata. Ta'aziyyar musamman ga Limamin Zamaninmu (AJ) da Jagoranmu (H). 

13/5/1444 (7/12/2022). 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post