SAI NA FA'DA!:- Babu Shakka Samun Nagartacciyar Uwa Ga 'Ya'Yanka a cikin Wannan Al’umma abu ne mai Matukar Muhimmancin Da Yakamata Maza su yi la’akari Da Shi Wajen Neman Aure_ Inji Fatima Adamu Tanja


 @MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE

Aure abu ne mai matuƙar muhimmanci a addinin Musulunci. Manzon Allah (S) ya faɗa cewa "A lokacin da ɗan adam ya yi aure, ya cika rabin addininsa". Sannan kuma Manzon Allah (S) ya ƙara da cewa: "Aure Sunnah ta ne, duk wanda ba ya tare da Sunnah ta ba ya tare da ni". Manyan dalilan da su ke sa wa a yi aure sun haɗa da:

-Domin ba wa maza da mata damar rayuwa tare cikin farin ciki da ƙaunar juna bisa dokokin addinin Musulunci.

-Domin a samar da ƴaƴa da gina al'umma tagari.

-Domin samar da haɗakar da shari'a ta amince da kuma kare mutunci da rayuwar al'umma daga kowane irin ƙasƙanci.

Daɗi da ƙari aure abu ne a tsakanin maza da mata domin ƙaunar juna da zamantakewa mai ɗorewa da samar da kykkyawan yanayin da za su tarbiyantar da ƴaƴansu su taso su na masu taƙawa da tsoron Allah. A wannan zamani da mu ke ciki mutuwar aure ta zama ruwan dare. Wannan dalili ya sanya ya zama lallai mu gujewa wannan mummunar ɗabi'a ta yawan mutuwar aure, mu zamar da gidajen aurenmu su zamto tamkar Aljannar Duniya. Babbar hanyar da za mu bi wajen kaucewa ruɗun wannan duniya shi ne mu sanya tsoron Allah a cikin zukatanmu.

Iyaye su na da muhimmiyar rawar takawa wajena taimako da ba da jagoranci da nusarwa ga ma'aurata. Akwai buƙatar su yi amfani da ƙwarewarsu da hikimarsu su nusar da su duk abin da ya dace game da wannan lokaci mai wahala na rayuwar aure. Su kuma ba su dukkan wani haɗin kai da goyon baya da gudunmawar da su ke buƙata ba tare da yin katsalandan kan abin da bai kamata ba.

Farkon aure abu ne mai matuƙar muhimmanci. Akwai buƙatar mu yi duk mai yi yuwa domin samun yardar Allah. Iyaye su tabbatar da Taƙawa a matsayin mahaɗi mai matuƙar muhimmanci game da auren ƴaƴansu. A wannan zamani wasu daga cikin iyaye idonsu ya rufe sun ruɗu da ruɗunin duniya, abin duniya su ke kallo wajen aurar da ƴaƴansu a madadin su maida hankali wajen yi wa ƴaƴa zaɓin abokan aure nagari. Da dama daga cikin iyaye su kan duba matsayin mutum a muƙami ko tarin abin duniya ko wata alfarmar duniya kafin ba da aure wanda hakan ne kuma ya ke haifar da mummunan zaɓi. 

♣ UWA TAGARI. 

Daga cikin muhimman abubuwa a Musulunci da suke taka muhimmiyar rawa ga tarbiyyar yara ita ce uwa, domin dukkannin wani tasiri da yaro yake samu to yakan samu a karkashin iyayensa, tasirin kan fara ne tun daga lokacin da aka dauki ciki har zuwa balaga.

Ruwaya ta zo daga jikan Manzo Imam Ja’afar Assadik daga Manzo (S) Ya ce “Farin ciki ya tabbata ga wanda mahaifiyarsa ta kasance kamammiya”.

Ka ga kenan samun Uwa tagari kamammiya me kyan hali da dabi’a yana da tasiri ga tarbiyyar yara. Idan aka samu uwa mai tausayi da hankali da Ilimi da sanin yakamata, wacce mijinta ke ganin girmanta da darajarta to wannan yana da tasiri a cikin tarbiyyar yara da halayensu.

Lallai idan uwa ta kasance mai daraja da kima a wajen mijinta to hakan zai samar mata da kwanciyar hankali da nutsuwa da zai taimaka kwarai da gaskiya wajen tarbiyyar yara, lallai uwa da ba ta samu wannan ba, to hakika za ta kasance kodayaushe cikin fada da ganin laifin kowa da huce haushi akan ‘yayanta, kuma yana iya sanyata la’ana ko zagin wadannan yara da zaluntarsu, wanda hakan zai iya haifar masu da mummunar al’ada da za su tashi da ita a rayuwarsu, kuma suna iya zama alakakai ga al’umma su zama tamkar wata guba a cikinta, ka ga rashin nutsuwa da kwanciyar hankalin ne ya yi tasiri a cikin rayuwar ’ya’yanta.

 
Babu shakka samun nagartacciyar uwa a cikin al’umma abu ne mai matukar muhimmancin da yakamata maza su yi la’akari da shi wajen neman aure, domin da mace tagari ne al’umma ke zama lafiya kuma abin alfahari da koyi ga kowa. 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post