Mu din Ga komawa Domin Ganin me Magabata suke Fada!!!



[ MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041 ]


Tun kana yaro kake Jin Ana cewa wannan Qaramin jirgin da yake yin Zane a sama can Qoli Qoli, wai jirgi ne da yake kai kaya qasar nijar!  Wasu suka ce a'ah idan jirgi ya 6ata ne ake tura shi yaje yayi wannan zanen idan ya wuce shi kuma jirgin da ya 6ace sai ya hango zanen ya biyo shi, 


Wadannan sune Misalin sharhin magabata Akan hadisan qarya!


 Banga dalilin da zai sa bayan Ka girma sai Ka nutsa cikin bincike Ka gano cewa ashe wancan jirgin ba Qaramin jirgi bane,  babbane kamar kowanne jirgi kuma dalilin da yasa yake yin wannan nisan high altitude, a sama shine, saboda jirgi ne wanda yake yin zirga zirga daga nahiya izuwa wata!  Wannan zanen da yake yi, hayaqin jirgi ne wanda yake fita kamar kowanne hayaqin jirgi kasancewar yayi nisa a sama har ya wuce in da iska take kadawa cikin sauri shi yasa hayaqin baya saurin bajewa domin yabi iska kamar yadda ba'a ganin hayaqin sauran jiragen da suke tashi a low altitude,  Sai kuma Ka dawo Ka fada mini cewa in a jiye wannan binciken, in duba in ga me magabata suka ce Akan wannan ilmin? Wato wancan sharhin da na fara a jiye Misalin sa a farko, 


A zancen gaskiya mu da muka zo a wannan zamanin mun fi duk wani magabaci yaqini da kuma ingantacciyar  hanyar tantancewa ko kuma sharhantar hadisan manzon Allah, zan kare iqirari na! 


Yadda Irin su haithami, su Ibn athir ko Ibn kathir da babban su Ibn hajar ko Ibn hadeed AL mu'utazali ko alqadhi iyal da sauran su birjik,  duk kan su babu wanda manzon Allah ya ruwaitar da hadisi a gaban shi kamar yadda muke,  sannan babu wanda sahabi ko tabi'i ya ruwaitar da hadisi a gaban sa kamar yadda muke a yau,  tsakanin su da su shekaru daruruwa ne, kamar yadda muke muma tsakanin mu da sharhin su shekaru ne daruruwa! 


Yadda suke da yan'cin sharhantar hadisai bisa yaqini haka haka su ma su Amirul Wa'izina suke da yan'cin yi, yadda sheikh Nasirudden Albani ya sharhanci littattafai na magabatan sa ya soke na soke wa, ya gyara na gyara wa ba'a tuhume shi da rena magabata babu dalilin da zai sa yanzu ku rinqa zargin mu da Rena magabata! 


Misali yadda suka sharhanci tare da sake sahhaha hadisin da ke cewa zafin zazza6i daga wutar jahannama yake Don haka ku sanyaya shi da ruwan zamzam,  wato duk mashayin zamzam yayi ban kwana da wutar jahannama ke nan? To koma dai yaya , mu kuma mun iya samun cewa daga malaria parasite yake! yanzu sai Ka ce mini in a jiye nawa ilmin in rungumi wancan sharhin da suka yi wa hadisin da yake tabbatar da cewa zafin Zazza6i daga wutar jahannama din yake? domin kawai wadancan manyan maluman da rawanin su baya qarya in kar6i wannan maganar da aka ce manzon Allah ya fada wanda shi kuma duk ilmin sa daga wajen Allah subhanahu wata ala yake,  in ga zancen yayi yamma haqiqar sa tayi Gabas, Sai Ka wai in rena ilmin Allah Don saboda in girmama magabata? Never, 


Yanzu hanyar da muka bi muka sake tantance hadisin da yake cewa wutar jahannama ta Roqi Allah cewa tana son ta dinga yin numfashi Sau biyu a shekara Allah ya yardar Mata! Wanda wai Numfashin farko shine lokacin zafi (bazara) numfashi na biyu kuma lokacin sanyi,  yanzu kana son sai in a jiye binciken kimiyya Akan juyawar yanayi,  in kar6i zancen tatsuniyar Numfashin wutar jahannama! 


Hanyoyin mu na kimiyyar zamani sun fi hanyoyin da magabata suka bi wajen tantance hadisai tunda da hanyar su tana da inganci fiye da tamu da hadisin saiyidina Abu huraira da yake cewa duniya Baza ta fi shekaru 270 bayan wafati ba, bai kufce ya iso har yau da wafati yake shekaru 1444 Ana karanta shi ! Hamer Ana Qarawa da sadaqallahul azeem ba!

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post