Kun Yarda Ku Birge Abokin Halitta Ku Saɓawa Mahaliccin Talikai Allah Ta'ala Ko?

 


Kashi Na Farko.


Amfanin Hankali Shine Tantanace Abu Me Kyau Da Mare Kyau‚ Ina Ne Hankulan Mu Suke Tafiya lokacin Da Zamu Aikata Wani Aiki? Mai Yasa Muke Aiwatar Da Wani Aikin Ba Tare Da Sanya Hankali Ba? Duk Da Allah Ta'ala Mai Rahama Ne Ga Bayin Sa‚ Isgili Ne Ga Allah Ta'ala Mu ’Yan Adam Mu Aikata Wani Abu Wanda Munada Yaƙinin Cewa Haramun Ne‚ Amma Sai Mu Biye Son Zuciyar Don Kawai Mu Birge Abokin Halittar Mu Wanda Bashi Da Wuta Bashi Da Aljanna.


Inason Jan Kunnen Mu Akan Yadda Muke Rusa Da’awar Allama Sayyid Zakzaky (H) Wanda Yayi Shekaru Yana Fafutukan Ganin Cewa Addinin Musulunci Shine Yake Iko Da Ƙasar Nan. Muna Kiran Kanmu Da Cewa Ma’abota Addini Ko? Eh! Ɗan Adam AKwai Rauni‚ Amma Ta Wannan Ɓangaren Ba Rauni Bane‚ Isgilanci Ga Allah Ta'ala Ne‚ Ka Burge Abokin Ka‚ Kin Birge Ƙawar Ki‚ Musamman Gake Mace Kin Tonawa Kanki Asiri Kin Zubar Da Mutumcin Ki Ki Sanya Hoton ’Yar’uwan Ki Mace A Media Ba Tare Da Sutura Mai Rufe Tsaraici Ba.


Abin Da Nake Ƙoƙarin Faɗa Shine‚ Sanya Hotunan Mata Amawa A “Social Media” Ba Tare Da Ƙyaƙyƙyawa Shiga Wanda Addinin Musulunci Ya Yarda Dashi Ba‚ Kuma Kaji ’Yar’uwa Tace Ai Itama An Turo Matane Ba Yadda Zatayi In Taƙi Sakawa Za Taji Haushi Ƙawar Tata Ba’amiya. Yanzu ‘Yar’uwa A Wannan Lokacin Fa Kin Samu Wani Damane Da Zaki Fahimtar Da Ita Cewa Hakan Kurkure Ne Ya Saɓawa Koyarwar Addini Da Mazhabin Ki‚ Ko Ba Komai Kinada Da Ladan Tinatar Da Ita Iya Rashin Kamun Kanta Wannan Nasiha Zaiyi Tasiri A Zuciyar Ta.


A Matsayin Ki Na “Sister” In Ki Biye Mata Ku Taru Ku Yaɗa Wannan Hoton Na Shigan Banza! Kun Samu Zunubi Ne Ko Lada? Ke Da Kisan Darajan Hijabi Ki Take Kinfi Kowa Zunubi Wurin Allah Ta'ala. Sheikh Adamu Tsoho Jos Yana Cewa; “Ya Kamata Muminai Su Sani Cewa Duk Wanda Ya Yaɗa Hoton Mace Ba Tare Da Hijabi Ba, Yana Da Kamasho A Cikin Zunubin Da Ta Aikata Na Rashin Cika Umurnin Allah (T) Kan Suturce Jikinta. Domin Ita Mace Dukkan Jikinta Al'aura Ne In Banda Fuska Da Tafukan Hannu. Kuma An Wajabta Mata Ɓoye Ado Da Sanya Hijabi Daga Dukkan Ajnabanta”.


 @22th December‚ 2022

©...Ibraheem Y. Ibraheem ✍️


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post