KU GAYIWA KOWA:- Dole A Cire Rubabbun Hadisai Daga Cikin Littafan Musulunci..!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


Duk Wanni Wanda ke amsa Sunan Malami a Kasar nan, Ya Fito yaga yiwa kowa...

ANNABI (S . A. W. W) YA FI KOWA TARBIYYA DA KYAWAWAN DABI'U


Zai iya zama cin mutunci ga Manzon Allah (S. A. W. W) a siffanta shi da aikata abinda yake yin hani a kansu, domin shi yafi cancanta da kiyaye dukkan abubuwan da ya hane mu aikata su.


Manzon Allah (S. A. W. W) yayi hani game da yin magana yayin da mutum yayi tsirara don biyan buqata, har yace Mala'iku na tsinewa wanda ke yin magana yayin da ya tube tufadinsa (dress). 


Wannan riwaya tasa malaman fiqhu suka fitar da Bani guda cikin littafan Fiqhu wanda ke bayani kan ladubba, kuma suka nuna haramcin yin magana a ban fadi (bath room) yayin da mutum ya cire tufafin dake jikinsa. 


Amma sai ga riwaya daga Bukhari kamar haka :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽



(357)- حدثنا إسماعيل بن أبي أويس قال: حدثني مالك بن أنس، عن أبي النضر، مولى عمر بن عبيد الله: 

أن أبا مرة، مولى أم هانىء بنت أبي طالب، أخبره: أنه سمع أم هانىء بنت أبي طالب تقول: ذهبت إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم عام الفتح، فوجدته يغتسل، وفاطمة ابنته تستره، قالت: فسلمت عليه، فقال: (من هذه) 


Isma'il Bn Abiy Uwais ya ce : Malik Bn Anas ya bani labari daga baban Nadhri, bararren bawan Umar Bn Ubaidullahi: Cewa baban Murrata bararren bawan Ummu Hani Bnt Abu 'Dalib ta ba shi labari cewa : Ya ji Ummu Hani Bnt Abu 'Dalib tana cewa :


" Na tafi wajen Manzon Allah (S.W .W. W) cikin shekarar da aka bude Makkah, sai na same shi yana wanka (a ban daki), 'yarsa Fatimatu kuma taba sitirce shi (da mayafinta). (Tace); Sai nayi masa sallama, sai yace :


" WACECE WANNAN  ?"


Sai nace : " Ummu Hani Bnt Abu 'Dalib ce. " Sai yace :


" MARABA DAKE YAA UMMU HANI.......... "


(BUKHARI, KITABUS-SALAH, 357)



Babban darasin da ake so a fitar cikin wannan riwaya shine, a tabbatar mana da cewa Annabi (S. A. W. W) na yin magana ko da kuwa yana cikin tsiraici . Yin hakan kuwa  zai iya zama abin zargi a kansa kamar yadda Allah (T) ke fada cikin Al-Qur'ani mai tsarki. 



يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لِمَ تَقُولُونَ مَا لَا تَفۡعَلُونَ (٢ )


كَبُرَ مَقۡتًا عِندَ ٱللَّهِ أَن تَقُولُواْ مَا لَا تَفۡعَلُونَ ٣ إ


" YAA KU WADANDA SUKA YI IMANI ! DON MENENE KUKE FADIN ABINDA BA KWA AIKATAWA.


YA GIRMA KUMA ABIN QYAMA A WAJEN ALLAH KU RIQA FADIN ABINDA BA KWA AIKATAWA ."


(Suratul-Saff :1-2)


Kenan suna tabbatarwa Annabi (S. A. W. W) aikata abinda yake yin hani a kansu, alhali shi yana aikata. 


A qarshe kuma shine su nuna cewa bai zama abin koyi ba tunda ba ya kiyaye abinda yake yin hani a kansu.


YAA ALLAH KA TSARE MU DAGA AMINTA DA IRIN WADANNAN MIYAGUN HADISAI 


🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


       (08137925034)


23rd December, 2022/  29th Jimada-Ulah, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post