Kishi ana yinsa ne wajen rigerigen tarairayar miji tare da bashi kulawa, bawai ana yin shi ne wajen cutar da abokan zama ba. _Nusaiba Ahmad Bauchi

 


MATA YE MASU IRIN WANNAN DABI'AR ALLAH YA SHIRYAR DASU..


Bai rage ki da komai ba, hakkokinki da na 'yayan ki duk Yana kokarin saukewa tare da kyautata miki.


Amma tsabaragen Hassada mijinki Yana da burin ya kara miki 'yar uwa sakamakon shi ya San kansa, kuma Yana da Halin yi, bai boyemiki ba Yana kuma da burin yin adalci a tsakaninku Amma ke tsabaragen Hassada kin daga hankalinki kince Sam bazai yiyuba, kece bin gidan Bokaye domin hana mijin ki ya Kara miki 'yar uwa wai a haka ke mai kishi..


Bayan kinsan Allah ne ya halastamasa yin mata (4). Amma  kin tada hankali tare ka bijerewa wa maganar Allah (T).


Kishi ana yinsa ne wajen rigerigen tarairayar miji tare da bashi kulawa, bawai ana yin shi ne wajen cutar da abokan zama ba.


Masu wannan dabi'a, hali kuji tsoron Allah, Allah (T) ya yaye musu, wadanda basa yi Allah ya kara farantawa a zamantakewar su🤲


7th_Dec_2022.

Real Nusaebeety.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post