Kada Kaji Tsoron Neman Macce Don Ba ka da Abun Aure !!

 


MACE ZA TA IYA FURTA KALMAR SO GA NAMIJI BA TARE DA YA FARA NUNA YANA SONTA BA  !!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


KADA KAJI TSORON NEMAN MACE DON BA KA DA ABIN AURE 


Cikin karin magana na malam Bahaushe yake cewa : " A RASHIN TAYI AKAN BAR ARHA. " Wani guri kuma yace : " TA HANYAR GWAJI JIRGI YA TASHI. " Lalle babu mai musu ko qaryata cewa : "RAGO BA YA SUNA A DUK INDA YAKE! "


Sau da yawa mutum na cin karo da wani abu wanda yake gani abin tsoro ne gare shi, amma in ya nuna halin jaruntaka sai ya zama shine abin tsoro wajen wannan abin. 
Ana samun mata ๐Ÿ‘ฉ ๐Ÿ‘ฉ  da yawa suga namiji ๐Ÿ‘จ  kuma suji sonsa ya kafu cikin qahon zuciyarsu, saboda wasu abubuwa da suka gani tare da shi na ilimi, kyakkyawar tarbiyya ko kuma tsananin riqonsa ga addini. A kullum za su riqa jin wannan son nasa na qara nutsewa cikin jinin jikinsu, amma saboda kunya ko girman kai sai ya hana su bijiro da kansu gare shi alhali ba sun sami wani wanda suka riqa a matsayin masoyi na aure ba. 


Nana Khadijah (S. A) za ta iya zama babban abin misali kuma abin koyi ga sauran matan muminai na duniya, domin ita ta fara nuna soyayyarta ga Manzon Allah (S. A. W. W) don ya zama abokin zama kuma Uba gurin 'ya'yanta.


Duk da cewa itama mai dukiya ce amma sai taga Annabi (S. A. W. W) ya fi mata (value) fiye da wannan dukiya da take dashi, saboda haka sai ta nuna tana sonsa da aure, shi kuma ya amsa mata saboda ta dace da shi. 


Darasi daga cikin wannan shine, duk da cewa dama Allah ya riga ya hukunta shine mijinta, amma da sai muce da ba don ta nuna tana sonsa ba da zai iya kubuce mata. Kenan idan ki kaga namiji wanda kike so, sai kuma ki kayi nawin baki ko ki kaji ji kunya, to, haqiqa za ki iya rasa shi. 


MATAR DATA NUNA SONTA GA ANNABI (S. A. W. W) 


Bayan Sayyidah Khadijah (S. A) an qara samun wata mata data nuna tana son Annabi (S. A. W. W), duk da cewa bai amince mata ba amma hakan bai zama qasqanci gare ta ba. 


Ga dai riwayoyin nan kamar haka :


๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ


ุนุฑุถ ุงู„ู…ุฑุฃุฉ ู†ูุณู‡ุง ุนู„ู‰ ุงู„ุฑุฌู„ ุงู„ุตุงู„ุญ(5120) - ุญุฏุซู†ุง ุนู„ูŠ ุจู† ุนุจุฏ ุงู„ู„ู‡: ุญุฏุซู†ุง ู…ุฑุญูˆู… ู‚ุงู„: ุณู…ุนุช ุซุงุจุชุง ุงู„ุจู†ุงู†ูŠ ู‚ุงู„: ูƒู†ุช ุนู†ุฏ ุฃู†ุณ، ูˆุนู†ุฏู‡ ุงุจู†ุฉ ู„ู‡، ู‚ุงู„ ุฃู†ุณ: 

ุฌุงุกุช ุงู…ุฑุฃุฉ ุฅู„ู‰ ุฑุณูˆู„ ุงู„ู„ู‡ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… ุชุนุฑุถ ุนู„ูŠู‡ ู†ูุณู‡ุง، ู‚ุงู„ุช ูŠุง ุฑุณูˆู„ ุงู„ู„ู‡، ุฃู„ูƒ ุจูŠ ุญุงุฌุฉ ؟ ูู‚ุงู„ุช ุจู†ุช ุฃู†ุณ: ู…ุง ุฃู‚ู„ ุญูŠุงุกูƒ، ูˆุงุณูˆุฃุชุงู‡ ูˆุงุณูˆุฃุชุงู‡، ู‚ุงู„ ู‡ูŠ ุฎูŠุฑ ู…ู†ูƒ، ุฑุบุจุช ููŠ ุงู„ู†ุจูŠ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… ูุนุฑุถุช ุนู„ูŠู‡ ู†ูุณู‡ุง ."


Bukhari yace : Aliyu Bn Abdullahi ya bamu labari : Marhum ya bamu labari yace : NA ji Sabitu Al-Bananiy yace : Na kasance a wajen Anas, kuma tare dashi akwai 'yarsa (zaune), sai Anas yace :


" Wata mata ta zo wajen Manzon Allah (S. A. W. W) tana bijiro da kanta gare shi (don ya aure ta), tace : " Yaa Ma'aikin Allah, kana da buqata dani (a matsayin wacce za ka aura) ?"


Sai ita 'yar Anas din tace : " Amma kunyarki ta yi qaranci, kin bada kanki (tozarta kanki) ! Kin bada kanki  !! " Sai (Anas) yace :


" Ai ta fi ki alkhairi  ! Ta yi kwadayin (auren) Annabi (S. A. W. W) sai ta bijiro masa da kanta (ta fara furta masa tana sonsa). "


(SAHIHUL-BUKHARI, KITABUN-NIKAH, BABIN MACE TA BIJIRO DA KANTA GA MUTUM SALIHI, HADISI MAI LAMBA :5120)


Cikin wannan riwaya za mu iya cewa ashe in ki kaga salihin mutum kika nuna kina sonsa, to, kinyi koyi da Nana Khadijah (S. A) kenan. 


A wata riwaya kuma an kawo magana ne yadda wani ya nuna yana son mata amma ba shi da abinda zai aure ta.  Ga riwayar kamar haka :


๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ


ุชุฒูˆูŠุฌ ุงู„ู…ุนุณุฑ


ู„ู‚ูˆู„ู‡ ุชุนุงู„ู‰ "ุฃู† ูŠูƒูˆู†ูˆุง ูู‚ุฑุงุก ูŠุบู†ูŠู‡ู… ุงู„ู„ู‡ ู…ู† ูุถู„ู‡" ุงู„ู†ูˆุฑ: 32 (5087) - ุญุฏุซู†ุง ู‚ุชูŠุจุฉ: ุญุฏุซู†ุง ุนุจุฏ ุงู„ุนุฒูŠุฒ ุจู† ุฃุจูŠ ุญุงุฒู…، ุนู† ุณู‡ู„ ุจู† ุณุนุฏ ุงู„ุณุงุนุฏูŠ ู‚ุงู„: 

ุฌุงุกุช ุงู…ุฑุงุฉ ุฅู„ู‰ ุฑุณูˆู„ ุงู„ู„ู‡ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… ูู‚ุงู„ุช: ูŠุง ุฑุณูˆู„ ุงู„ู„ู‡ ุฌุฆุช ุฃู‡ุจ ู„ูƒ ู†ูุณูŠ، ู‚ุงู„: ูู†ุธุฑ ุฅู„ูŠู‡ุง ุฑุณูˆู„ ุงู„ู„ู‡ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… ูุตุนุฏ ุงู„ู†ุธุฑ ููŠู‡ุง ูˆุตูˆุจู‡، ุซู… ุทุฃุทุฃ ุฑุณูˆู„ ุงู„ู„ู‡ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… ุฑุฃุณู‡، ูู„ู…ุง ุฑุฃุช ุงู„ู…ุฑุฃุฉ ุฃู†ู‡ ู„ู… ูŠู‚ุถ ููŠู‡ุง ุดูŠุฆุง ุฌู„ุณุช، ูู‚ุงู… ุฑุฌู„ ู…ู† ุฃุตุญุงุจู‡ ูู‚ุงู„: ูŠุง ุฑุณูˆู„ ุงู„ู„ู‡، ุฃู† ู„ู… ูŠูƒู† ู„ูƒ ุจู‡ุง ุญุงุฌุฉ ูุฒูˆุฌู†ูŠู‡ุง، ูู‚ุงู„: (ูˆู‡ู„ ุนู†ุฏูƒ ู…ู† ุดูŠุก)
Game da fadinSa (S. W. A) : " IDAN KUN KASANCE FAQIRAI ALLAH ZAI WADATA KU DAGA FALALARSA. "


Bukhairi yace : Qutaibata ya bamu labari : Abdul-Azeez Bn Abiy Haazam ya bamu labari daga Sahl Bn Sa'eedil-Saa'idiy yace:


" Wata mata ta zo wajen Manzon Allah (S. A. W. W) sai tace : " Yaa Ma'aikin Allah, na zo ne na bayar da kaina (kyauta) gare ka (ka aure ni). " (Sahal) yace : " Sai Manzon Allah (S. A. W. W) ya kalle ta (sama-da-qasa), ya qara kallonta. Sa'annan ya sunkuyar da kansa qasa (ba tare da ya ce mata wani abu ba). A yayin da matar taga cewa ba zai biyo mata buqatar wani abu ba (game da manufa tata) sai ta zauna. Sai wani mutum daga Sahabbansa ya miqe yace :


" Yaa Ma'aikin Allah, idan dai kai ba ka da buqata zuwa gare ta, to, ka aurar min da ita. " Sai (Manzon Allah (S. A. W. W) yace :


" SHIN, TARE DA KAI AKWAI WANI ABU (wanda za ka bata a matsayin sadaqi ?"(BUKHARI, KITABUN-NIKAH, BABIN AUREN WANDA KE CIKIN QUNCI, HADISI MAI LAMBA :5087).


Akwai cigaban wannan hadisi amma an datse shi, domin anyi bayanin yadda akayi har wannan Sahabi ya auri wannan mata da sadaqin wasu surorin Qur'ani a matsayin sadaqi ba kudi ko kaddara ba. 


Ga cikakkiyar riwayar nan mun kwafota daga wani littafin cikin harshen turanci. A cikin za kuga yadda al'amarin ya kasance. 


๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ๐Ÿ‘‡๐ŸฝNarrated By Sahl bin Sad As-Sa'idi:

 " A woman came to Allah's Apostle and said, "O Allah's Apostle! I have come to give you myself in marriage (without Mahr)." Allah's Apostle looked at her. He looked at her carefully and fixed his glance on her and then lowered his head. When the lady saw that he did not say anything, she sat down. A man from his companions got up and said, "O Allah's Apostle! If you are not in need of her, then marry her to me." The Prophet said, "Have you got anything to offer?" The man said, "No, by Allah, O Allah's Apostle!" The Prophet said (to him), "Go to your family and see if you have something." The man went and returned, saying, "No, by Allah, I have not found anything." Allah's Apostle said, "(Go again) and look for something, even if it is an iron ring." He went again and returned, saying, "No, by Allah, O Allah's Apostle! I could not find even an iron ring, but this is my Izar (waist sheet)." He had no rida. He added, "I give half of it to her." Allah's Apostle said, "What will she do with your Izar? If you wear it, she will be naked, and if she wears it, you will be naked." So that man sat down for a long while and then got up (to depart). When Allah's Apostle saw him going, he ordered that he be called back.


When he came, the Prophet said, "How much of the Qur'an do you know?" He said, "I know such Sura and such Sura," counting them. The Prophet said, "Do you know them by heart?" He replied, "Yes." The Prophet said, "Go, I marry her to you for that much of the Qur'an which you have."๐Ÿ‘†๐Ÿผ๐Ÿ‘†๐Ÿผ๐Ÿ‘†๐Ÿผ๐Ÿ‘†๐Ÿผ๐Ÿ‘†๐Ÿผ๐Ÿ‘†๐Ÿผ๐Ÿ‘†๐Ÿผ๐Ÿ‘†๐Ÿผ๐Ÿ‘†๐Ÿผ๐Ÿ‘†๐Ÿผ๐Ÿ‘†๐Ÿผ๐Ÿ‘†๐Ÿผ๐Ÿ‘†๐Ÿผ๐Ÿ‘†๐Ÿผ๐Ÿ‘†๐Ÿผ๐Ÿ‘†๐Ÿผ


To, idan wannan riwaya ta inganta sai muce lalle ko da ba ka da kudin aure in har kaga mace wacce kake sonta za ka iya tsayawa, idan rabonka ce sai kaga ka samu, domin Allah babu abinda bai iya ba. 


Akwai wasu iyaye wadanda suke da wadata  kuma burinsu shine suga 'ya'yansu sun sami mazaje nagari ba 'yan garari ba.  Saboda haka in har sun yabawa mutum za su iya aurar masa har ma tu taimaka masa da jari ko dora shi kan wata harka don ya sami abinda zai riqe musu 'yarsu cikin mutunci. 


Kaga idan kaci karo da irin wannan sai ka sami mata cikin sauki, kai kuma sai ka riqe amana ka mutuntata tare da mahaifanta. 


YAA ALLAH KA HADA MU DA RABONMU, DOMIN NIMA INA SON QARA WATA MATAR AMMA BANI DA KUDIN AUREN  !


๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ๐Ÿ™๐Ÿผ


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍๐ŸผAdo Isah Guda.


          (08137925034)


2nd December, 2022/ 8th Jimada-Ulah, 1444.2 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Elahee bihaqqi musdhafal adhar, amman samun irin wadan nan matan a zamanin nan akwai wuya sai dai in kana da rabo allah ta'ala ya hadamu da alkhairi.

    ReplyDelete
  2. To alhmdllh Allah yasa mudace Allah yabada kowa da rabonsa

    ReplyDelete
Previous Post Next Post