Hukumar Lafiya ta Duniya ta lissafa abubuwa 7 da za su faru da zarar daina shan taba sigari:!!!

 


@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@


1. Bayan mintina 20: Hauhawar jini da saurin bubbugawar zuciya za su ragu.


2. Bayan awanni 12: Gurɓatacciyar iskar nan mai guba (carbon monoxide) za ta daidaita a cikin jini.


3. Bayan sati 2 – 12: Zagayawar jini da aikin huhu za su haɓaka.


4. Bayan wata 1 – 9: Tari da gajercewar numfashi za su ragu.


5. Bayan shekara 1:  Haɗarin samun cutar jijiyoyin jini da ke bai wa zuciya jini zai ragu da rabi.


6. Bayan shekara 5: Bayan shekara 5 – 15 da ƙaurace wa shan taba sigari, haɗarin kamuwa da shanyewar ɓarin jiki zai yi daidai da na wanda bai taɓa sha ba. 


7. Bayan shekara 10: Afkuwar mutuwa daga cutar daji / kansar huhu za ta ragu zuwa rabi. Haka nan, haɗarin kamuwa da cutar dajin / kansar baki, maƙogaro, mafitsara, ƙoda da matsarmama za su ragu.


Ƙaurace wa shan taba a yau!

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post