GANDUJE ZAI SA HANNU KAN HUKUNCIN RATAYE ABDULJABBAR


Kwamishinan Shari'a ya ce Ganduje na kan bakarsa game da sanya hannu kan hukuncin rataya da kotun Musulunci ta yanke wa Abduljabbar Kabara kan batanci…

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce yana kan bakarsa game da sanya hannu kan hukuncin rataya da kotun Musulunci ta yanke wa Abduljabbar Kabara kan batanci ga Manzon Allah (SAW).

Kwamihinan Shari’a na Jihar Kano, Lawan Musa, ne ya sanar da haka, bayan Aminiya ta tuntube shi kan hukuncin da Babbar Kotun Musulunci ta yanke wa malamin da gwamnatin jihar ta gurfanar kan zargin batanci.

Ya ce, “Matsayin gwamna bai sauya ba kan sanya hannu a kan wannan hukunci, kamar yadda matsayin bai sauya a kan hukuncin Kisan Hanifa ba.

“Akwai matakan da ya kamata a bi kuma a shirye Mai Girma Gwamna yake; da zarar an kawo zai sanya hannu a kai,” in ji shi.


Kwamishinan Shari’an ya kara da cewa, “Babu wanda za a bari ya taka doka, kuma an dauki duk matakan da suka kamata.

“Mun gurfanar da Abduljabbar a gaban kotu ne domin ba shi duk wata dama ta kare kansa, kuma Alhamdulillahi kou ta gamsu gamsu da hujjojin da muka gabatar a kansa, sannan ta yanke masa hukuncin da ya cancanta.”

A cewarsa, hukuncin kotun ya wanke gwamnatin jihar kuma ya nuna babu wani shafaffe da mai, sannan gwamnatin ta dauki duk matakan da suka dace na tabbatar da doka da oda.

-Aminiya

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post