Ganduje ya kori Baba Impossible daga muƙamin sa na kwamishinan harkokin addini a Jihar Kano...!!!

 



@MA'ASUMAH TV// Mnnu/Ng0041@

Aliyu Samba 


Gwamnatin Jihar Kano ta sauke kwamishinan harkokin addini na jihar Kano, Dr. Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible) daga mukaminsa.


Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 31 ga watan Disamba, ya ce an cire Kwamishinan nan take cikin gaggawa.


Ya ce korar kwamishinan ya biyo bayan halin rashin da’a da yake nuna wa a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati mai rike da mukami, da kuma kalamai da yake furtawa marasa kan gado.


Malam Garba ya bayyana cewa, an kuma same shi yana gudanar da al’amuran ofishinsa kamar aikin da ke mallakin sa, har ma yana rage ranakun aiki ga ma’aikatan ma’aikatar, inda ya cire ranakun Laraba da Juma’a.


Malam Garba ya kara da cewa, Baba Impossible baya ga gudanar da aiki gaba gaɗi ba tare da tuntubar wadanda ya dace ya tubtuɓa ba, Baba Impossible baya biyayya ga gwamnati.


Ya kara da cewa tuni Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya aikewa majalisar dokokin jihar sunan wani da ya zaba wanda zai maye gurbin sa, Dakta Nazifi Ishaq Bichi na Jami’ar Bayero Kano a matsayin sabon kwamishinan Harkokin Addini na jihar Kano.


Sanarwar ta kara da cewa, gwamnan ya yi fatan alheri ga korararren kwamishinan.


Jarida Radio

31/12/22

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post