Duniyar Mutuwa Kashi na(1)...!!!


  
@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE


{Rubutawa Ml. Adam Abu Umayrah} 

Dukkan yabo da godiya da kowane irin nau'i nakirari da girmamawa sun tabbata ga Allah madaukakin sarki Ubangijin rannan da shekaran jiya da jiya da yau da gobe da ranar da bata zoba, Ubangijin daya halicci Annabi Adam (a.s) ba Uwa ba Uba, kuma ya halicci Annabi isah (a.s) ba Uba. 

Ya Allah ka dada tsira da Aminci, da soyayya da salati zuwa ga farin jakada wanda ka aikoshi zuwa ga mutane da Aljanu, wato Shugabanmu kuma manzon ka(Annabi muhammad,{saww}) da Iyalan gidanshi tsarkaka, da sahabbai da tabi'ai wadanda suka bishi da kyautatawa har izuwa ranar Alqiyama. 

Bayan haka wannan darasi yana koyar damu Rayuwar mu tanan gaba wato; Rayuwa bayan mutuwa, Allah yasa mudace. 

Adaya daga cikin tafiye tafiyena zuwa birnin Riyaad, nai shirin zuwa filin jirgin sama kafin lokacin tashin jirgin da awa 1, sai dai cunkoson hanyar, da kuma bincike yasa na makara a tafiyata, sai na dinga sauri har na isa wajen tsayuwar motoci, sai na dauki kaati na(Visa) da sauri, nai parking mota ta a wurin da ni bansan shin wurin parking din ma aikatane ko na matafiya, nide nasauqo da sauri daga cikin mota nadauki jakaata ahannuna, nashiga tafiya(Escalator)na isa dakin bincike, nacire dik abinda ke aljihuna nariqe a hannuna,na danna naqurar bude qofa amma sai naji sanarwa wai ajikina akwai wani abu d bazan iya wucewa da shiba, sai nashiga damuwa, caan sai natina agogona ne ai, sai nacire nasake danna na'urar, sai ta bude nawuce lpy, 

Na isa wajen jirgin da sauri, Nace; Ni matafiyine zuwa Riyaad, cikin jirgin mai lamba 1411, sai ma aikacin yace Ai jirgin ya cika, sai nace dashi dan Allah kataimakamin ina da Alqawari ne wanda ba makawa in halarceshi a wannan daren, sai yace; kada ka yawaita magana dan jirgin yariga ya cika, kuma babu wanda zai daga maka qafa, Sai nace; Hasbiyallah!. 

Na fito daga wajensa,, Ina tsaye ina kallon jirgin bani da tsimi bare dabara face ga Allah, sai tunanin yadinga ketomin akaina cikin sauri! Shin zanbar tafiyar nanne? Kodai intafi a mota? Ko indauki hayar mota intafi? Aqarshe zuciyata tabani natafi amotar haya, sai nakoma bangaren 'yan tasi(taxi), sai nasamu wani mutum cikin sabuwar mota, (Camry) nace dashi nawa zaka kaini Riyaad?. 

Yace; Riyal 500! Nai qoqarin samun ragi a wajensa amma bai rage komaiba illah riyal 50, Na hau motar nikadai nace dashi yayi sauri, domin dolene naisa Riyaad cikin wannan dare. 

Ni bansaniba Ashe qarshena cikin awannine , Yace dani shakuruminka zanyi gudu dakai tamkar tsuntsu, ai kuwa haka akai, yadinga gudu na hauka, don namasa alkawari idan ya isa Riyaad dani kafin isha'i, zan bashi qarin kyautar Riyal 100(baya ga 450)muna tafe muna hira yana tambayata, ina tambayarsa muna raha, dan de mudebe kewar juna,kwatsam sai mahaifiyata tafadomin akwakwalwa akan naqirata, aikuwa naqirata, tace; Ina kakene ya Aba saarah? Sai nabata labarin jirgin da yadda na rasa tafiya ta jirgin, sannan yanzu nahau mota ne don tafiyar, sai tayi shiru, wanda hakan yajanyo hankalina, sai mahaifiyata tace; kai d'aana Allah ya kareka daga sharrin abindake boye, sai nace Ameen, zanqiraki dazarar na isa insha Allah, kina da wasiyya garenine? Sai Tace;kasancewarka lafiya har tsawon rayuwat, Anan muka kammala waya da ita. 

Sai naji wani abu araina, nakejin wani abin Al ajabi na shirin Aukuwa dani! Sai naqira matata tace, Bani labarinka ya rayuwata,  kilomita nawa kukai? Nace;  Yanzu munyi kilomita 150. 

Tace; Wallahi munyi rashinka, in baka gidannan duk babu dadi! Nace; Allah ya miki Albarka, in Allah yaso inanan dawowa ajirgin raana, ki kula da yarana, Ki sumbacemin susu, Allah ya kula mana da ita!. 

Tace; Albishirinka, ai tun da tadawo tace Ina Baba? Nace; bani ita! Susu tace; Baba ina kake  Nace; Susu nan bada jimawaba zan dawo muku insha Allah, muka danyi dariya nace to ba mama wayar, sai ta bata, Nace; kina da wata wasiyya ne agareni? Tace; Faatana shine kubutar rayuwarka!

Ban saniba menene dalilin da yasa damuwata ta soma tsananta agareni! 

Nashiga zurfin tinani wanda bandawo ba sai ji nayi Direba na Tambayata yace; Shin yaranka nawane? Nace mar 4,2 maza, 2,mata yace Allah yashiryarmaka dasu nace; Ameen, kaima haka. 

Nakalli hanya, sannan nakalli sama Ina kallonta, nakalli rana, sai naga kadan yarage ta fadi, nafadi ina mai qure kallo; Ya Allah Rahmarka nake kwadayi ya Rahman. 

Ban Auneba naji direba na neman izinina yana so yasha sigari, sai nace; Ya kai dan uwana, kai mutum ne me daraja, kuma ina tsammanin tattare dakai akwai alkhairi mai girma, ya zaka yardarwa kanka kaqona kanka? Ka koqone kudinka kuma katauye Addininka a dalilin sigarii?,  Kuma qarshe bata amfanarka saide cutar dakai, sai yace; Yaa kai dan halal, kamin Addu'a, Wallahi nayi qoqarin barin shan ta cikin Ramadhan da yagabata amma na kasa, Sai nace dashi; kai mutum ne da Allah yabashi iko amma kakasa akan sigari, nacigaba damar nasiha, da shiryar dashi, shi kuwa yana saurarena yana mai nadamar shan sigari dayakeyi, bayan kammalawata sai yace ; Insha Allah bazai sake shan sigariba, Nace masa inamai farin ciki! Allah ya tabbatar damu akan addini. 

Zan iya tina cewa najingina kaina ajikin motar ina tinani narasa me yake sani firgici, narasa akan menen gashi inajin damuwa me tsanani awannan yanayi, kwatsam sai jin qara mai tsanani nai dani da direba dik muka rikice, nadauka cewa tayace ta fashe sai nacemar karage sauri kasanya alamar (signal) don sauran motoci susan munsamu matsalane, shi kuwa, ko magana baya iyawa, ya kankame stiyaarin motar, alamun damuwa cike da fiskarsa, lokaci qanqani motar ta hantsila bangaren dama(tabi wrong way) ta dinga gundun balaa, nide Allah ya taimakeni, ina ta fadin("Laa ilaha illallah Muhammadur Rasulillah") inajin kamar ina daga muryata da itane, Chan sai ga wani mutum ya zomin cikin tsananin duhu da nake gani, yazo min da gemuna fari fat, yace dani; Yaa 'Dana wannan itace qarshen rayuwarka kuma nazo makane ina mai maka nasiha kafin kahadu da Ubangijinka, Haqiqa na san ka, kai mutum ne mai hazaaqa, kana son Alkhairi, dan haka da sannu zanmaka wasiyya da wata wasiyya, domin Allah ne ya aikoni wajenka. 

   Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un....

{Muhadu a kashi na 2, Insha Allah}. 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post