Dubban Musulmi ne suka Halarci muzaharar Release Zakzaky Passport a garin KadunaDa Yammacin Yau Litinin Ne Yan uwa Almajiran Sayyid Zakzaky (H) Na Dairan Kaduna suka gudanar da Gagarumin Muzaharan kira ga Gwamnatin Buhari ta sakar ma Sheikh zakzaky da matarshi Fasfo din su domin suje neman lafiya. 


Muzahara wanda aka fara daga kan Levintis dake tsakiyar cikin Garin kaduna. 


Daruruwan Yan uwa maza da mata ne suka fito muzahara suna rere wake na kira ga Gwamnatin ta sakar ma Sheikh zakzaky da Mai dakinsa fasfo din su domin suje nema lafiya. 


Muzaharan tayi Nisan gaske har zuwa inda aka kulleta an fara Muzahara lafiya an kuma tashi lafiya. 


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post