Daga cikin Jawaban Shaikh Ibraheem Zakzaky yanzu haka karfe 2:24pm

 


Tunawa da waki'ar Buhari a Abuja a yau: yanzu haka Shaikh Ibraheem Zakzaky ke gabatar da jawabin rufewa.


Waki'ar Zariya ya shiga kundin tarihin kasarnan


Waki'ar Buhari mun rubuta da tawadar da ba ta bushewa da kuma allon da ba ya goguwa, wato zukatanmu ke nan.


Manufar waki'ar Zariya shi ne ba kawai a shafe mu ba (jikkunanmu), a ma shafe da'awarnan ta ambaton a koma wa tafarkin Allah baki daya.


Mu al'umma ne da ba ta hanyar jini muka zama al'umma ba, ta hanyar i'itikadi ne, ba zai yiwu a shafe mu ba. 


abin da suka yi (a Zariya a Disambar 2015) ko Fir'auna bai yi ba, domin Fir'auna 'ya'ya maza jarirai ya rika kashewa lokaci bayan lokaci. Abin da suka yi mana a Zariya sun kashe kowa da kowa, mata da jarirai, kowa da kowa e aka kashe. Wanda shi Fir' auna ba kowa ya kashe ba. A tarihin ba mu ta6a sanin wani abu irin wannan ba. 



idan na ce abin da suka yi dabbanci ne, na ci zarafin dabba. Ita dabba tana kisa ne ko don tana fuskantar hadari ko don yunwa, kamar Zaki. Dabbobi ba su kisa saboda kisa. Wannan kisa aka yi saboda kisa. Aka rutsa mu kwanaki uku a jere ana kisa dare da rana. Kisa ne na mugunta. Ana watsa wa mutane fetur ana kona su.


Haka suka yi a Husainiyyah Bakiyyatullah da Gyallesu, suna zubawa mutane mai suna cinna musu wuta, mutane da ransu. Bayan kona kutane da wuta, an bizne mutane da rai.


An kuma kona gawarwaki. Ba su kyale ba, har kaburburan wadanda aka kashe mana, sun bi sun kona. Suka zauna wata guda cur a makabarta din, sanan suka tashi suka bar kaburburan a bude.


sun aikata abubuwan da dan Adam ba zai iya sawwalawa ba.


A Darur Rahma, akwai Rakuma, Shanu, Awakai, da Kaji suka karkashe suka kwashe wasu.


Sun tare mutane a hanyar Katsina da Kano da Kaduna da dukkanin hanyoyin dake shiga Zariya suka yi ta kisa.


sun dade suna shirin yadda za su rutsa mu duk su karkashe mu a ji shiru.


*ba za mu ce muku ka da ku yi abin da kuka nufa ba, kullum tunaninsu yadda za su kashe mu ne ko su rusa gine-ginenmu, shi ke nan an gama. Haka suke tunani. Sun yi abin da suka yi. Amma sakamako na nan zuwa.


yau shekara bakwai da wannan waki'a, bayan waki'ar sun rika bude wuta kan kowanne munasaba ba tare da la'akari da munasabar ba. 


Duk a cikin jawaban Shaikh Ibraheem Zakzaky dake gudana yanzu haka a birnin Tarayya Abuja a yayin taron tunawa da waki'ar Buhari karo na bakwai.


Kundin Tarihin Harka

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post